Kai Shugaban Kasan Nigeria ne, ba Shugaban Fulani ba – Gwamnan Jahar Benue ga Shugaba Buhari

 

Shugaban kasa yayi alkawarin cewa zai kasance na kowanni dan Nigeria, cewar Ortom.

Gwamnan ya bayyana haka a wani taron manema labarai.

Yace amma shugaban ya kasance kamar na makiyaya ne kawai Gwamnan jahar Benue, Samuel Ortom, yace shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi alkawarin kasancewa na kowanni dan Nigeria, amma abinda ke nuni kamar shi na Fulani makiyaya ne kawai.

A wani jawabinsa yayin amsar mulki a 2015, Shugaban yayi alkawarin kasancewa “Ni na kowa ne, kuma ba na kowa ba”.

A wani tattaunawa da manema labarai a Makurdi ranar Laraba, gwamna Ortom yace babu abinda yake nuni ga shugaban yana jagorancin duk yan Nigeria ne, rahoton The Cable.

Gwamnan ya kara da cewa yan jahar Benue ba bayin fulani bane.

“Ya Shugaban kasa, idan kana jina, ina so na sanar da kai cewa ka yiwa duk mutanenka yan Nigeria alkawarin adalci , kamar yadda The Punch ta ruwaito yana cewa.

“Kace zaka kasance na kowa ba na kowa ba, amma yanzu yayi nuni cewa kai na fulani ne kawai, saboda babu abinda yake zuwa daga gareka wanda zai sa mutane su ji ajikinsu kai shugabansu ne.

“Kai Shugaban kasan Nigeria ne, ba Shugaban Fulani ba.”

“Kai shugaban kowa ne kuma inaso ka sani a matsayinka na mai ruwa da tsaki na wannan kasa, kasani cewa abinda yake faruwa bashi da kyau kuma hakan yana iya sanya rabuwar kai a kasar.

Gwamnan yace ya bukaci gwamnatin tarayya ta yarje lasisin bindigar AK 47 ta yadda yan Nigeria zasu iya kare kansu.

“Shi yasa nayi kira ga gwamnatin tarayya akan ta bani da wasu lasisin rike bindigar AK 47. Saboda idan ina da AK 47, sai ga bafulatani, yasan ina da shi yana dashi, shikenan sai mu fuskanci juna,” yace.

“Amma baza ka iya hanani makami kaba bafulatani ba.Wannan ba adalci bane, gwamnatin tarayya tana da san kai.

duk rashin tsaron da ake fama dashi gwamnatin tarayya ce ta ja.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here