Shugabannin da Suka yi Nasara a Zaben Jam’iyyar APC
Wasu ba su samu yadda suke so a wajen zaben shugabannin jam’iyyar APC na kasa da aka yi ba.
Daga cikin wadanda sakamakon zaben ya yi masu kyau dai akwai mafi yawan gwamnonin jihohi.
An tsaida ‘yan majalisar NWC na jam’iyyar APC ne ta hanyar maslaha ba tare da an kada kuri’a ba.
A wannan rahoto da aka fitar, TheCable ta bi sakamakon zaben da aka yi, ta yi nazari a kan wadanda suka yi dace, da wadanda ba su yi nasara ba:
Buhari ya tashi da shugaban APC
Kamar yadda ku ka samu labari, Sanata Abdullahi Adamu ne wanda zai rike shugabancin jam’iyya bayan kan daukacin ‘yan APC ya hadu a kan sa.
Mai girma Muhammadu Buhari ne ya nunawa gwamnoni cewa yana tare da Sanata Adamu. Hakan na nufin a nan shugaban kasa ya samu yadda ya so.
Osinbajo yana kallon ikon Allah
A zahiri babu wani ‘dan takarar da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo yake goyon baya a zaben na jam’iyyar APC da aka yi shirya jiya a Abuja.
Kusan har zuwa yanzu Osinbajo bai da ta-cewa a jam’iyyarsa ta APC mai mulki. Saboda haka ba za a ce ya ji kunya ko kuma ya yi nasara a zaben da aka yi ba.
Tinubu ya tsira da kujera a NWC
Read Also:
Jaridar ta ce Bola Ahmed Tinubu ya rasa kujeru biyu daga cikin wadanda aka warewa yankinsa a NWC. Amma ya tashi da kujerar shugaban matasa na kasa.
Gwamnonin APC na kudu maso yamma sun yi nasarar kawo Iyiola Omisore da Isaac Kekemeke a maimakon Ife Oyedele da Bolaji Repete da Tinubu ya ke so.
Takarar Amaechi za ta kai labari?
Duk da Ministan sufuri na kasa, Rotimi Amaechi bai bayyana niyyar tsayawa takara ba, ana zargin yana cikin wadanda suke hangen kujerar shugaban kasa.
Amaechi ya ki bayyana wanda yake goyon baya a zaben. Daga jiharsa dai Victor Gladom ya yi nasara. Amma ana tunanin nasarar Adamu ta yi masa dadi sosai.
Gwamnonin APC sun samu ganima
Abdullahi Adamu ne kadai ya sha a cikin ‘yan takarar shugaban kasa. Hakan yana nufin mafi yawan gwamnoni sun samu yadda suke so a sauran mukamai.
Amma ana kukan irinsu Kano da ke da karfi a APC ba su samu manyan mukami a NWC ba musamman da Suleiman M Argungun ya doke Ismail Ahmed.
‘Yan takarar Buhari sun sha kashi
Kun ji cewa daga cikin wadanda shugaban kasa ya so su samu kujera a NWC akwai tsohon shugaban majalisar dattawa, Ken Nnamani wanda bai kai labari ba.
Haka zalika akwai Farouk Adamu Aliyu wanda ya dade yana tare da Buhari. Wani ‘dan takarar fadar shugaban kasa da aka kifar a zaben shi ne Arc. Waziri Bulama.