Yadda Kasar Sin Ke Yiwa ‘Yan Kasar Gwajin Cutar Sarkewar Numfashi

 

Gwamnatin kasar Sin ta fara yiwa mazauna Beijing gwajin Korona ta dubura.

Ana bukatar tura auduga cikin duburan mutum na tsawon inci daya.

Za’a juya audugar ciki akalla sau biyu cikin dakikai 10 sannan a cire.

Masana sun bayyana cewa gwaji ta wannan hanyan ya fi bada sakamako na kwarai.

Kasar Sin ta fara yiwa al’ummarta gwajin cutar Korona ta hanyar tura auduga cikin dubura, wannan wata hanya ce da masana sukace tafi basa sakamako na kwarai, Daily Mail ta ruwaito.

Domin yin wannan gwaji, ana bukatar tura audugar cikin dubura na tsawon inci daya zuwa biyu kuma a juyashi.

Bayan yin haka sau biyu, za’a cire audugar sannan ayi gwaji.

Mahukunta a birnin Beijing sun fara wannan gwajin ne bayan kamuwar da wani yaro dan shekara 9 yayi da cutar Korona makon da ya gabata.

Wani masani a asibitin You’an dake Beijing, Li Tongzeng, yayin hira da tashar CCTV ranar Asabar, yace an gano kwayoyin cutar Korona sun fi dadewa cikiin dubura fiye da baki da hanci.

“Mun samu cewa wasu masu cutar Korona da basu nuna alamu suna warkewa da wuri. Akwai yiwuwan ba za’a samu cutar a makogwaronsu ba cikin kwanaki uku zuwa biyar,” Li ya bayyana.

“Amma cutar ta fi dadewa a samfurin da aka dauka na ba hayan mutum, idan aka hada da wadanda aka dauka daga wuraren irinsu baki, hanci da makogwaro.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here