Gwamnatin Tarayya ta Fara Raba Tallafin Kudi ga Matan Jahar Kaduna

 

Gwamnatin tarayya ta fara raba wa matan jahar Kaduna kudin tallafi N20,000.

An bayyana cewa, za a tallafawa matan ne a fadin kananan hukumomi 23 a jahar Kaduna.

Gwamnatin jahar Kaduna ta yabawa gwamnatin tarayya na yunkurin tallafawa mata.

Gwamnatin tarayya ta fara raba wa matan karkara kudi Naira dubu 20 a karkashin shirin bayar da tallafi ga matan karkara 4,000 a jihar Kaduna, Daily Trust ta ruwaito.

A cewar gwamnatin tarayya, za a zabi matan 4,000 a fadin kananan hukumomi 23 na jahar.

An gabatar da shirin a cikin shekarar 2020 don ci gaba da aiwatar da tsarin zamantakewa a Gwamnatin Shugaba Buhari.

Babban Sakatare, Bashir Nura Alkali, ya wakilci Ministar jin kai da Harkokin Ci Gaban Jama’a a taron bude shirin da aka gudanar a Jihar Kaduna.

Ya bayyana cewa “ya yi daidai da hangen nesa game da kasa na Shugaba Muhammad Buhari na fitar da ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci cikin shekaru 10.

Ya ce an tsara shirin ne don samar da tallafi sau daya ga wasu mata masu karamin karfi da masu rauni a yankunan karkara da birane na kasar.

“Za a raba tallafin kudi na N20,000.00 ga mata masu karamin karfi kimanin 125,000 a fadin Jahohi 36 na Tarayya da Babban Birnin Tarayya.

“Burinmu a Jahar Kaduna shi ne bayar da tallafin ga sama da mutane 4,000 a fadin kananan hukumomin 23.” inji shi.

A nata jawabin, mataimakiyar gwamnan jahar Kaduna, Hadiza Balarabe ta ce “COVID-19 har yanzu yana yin mummunan tasiri a rayuwar mutane musamman mata.

Ta ce bayar da kudin babu shakka zai kawo taimako ga mata a cikin al’umma, musamman wajen karfafa kudaden shigansu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here