Rundunar Sojin Najeriya ta Sake Ceto ‘Yan Matan Chibok Biyu a Borno

 

Rundunar sojin Najeriya sun samu nasarar ceto wasu ‘yan mata biyu daga cikin ‘yan matan Chibok da aka sace.

A baya an ceto wasu ‘yan mata biyu daga cikin ‘yan matan Chibok da ke hannun Boko Haram tsawon shekaru sama da takwas.

Kungiyoyin ta’addanci a Najeriya sun sha sace dalibai, tun bayan da kungiyar ta fara sace ‘yan mata sama da 100 a Borno.

Bama, Borno – Akalla shekaru takwas bayan kai mummunan hari Chibok da kuma sace ‘yan mata a wata makarantar sakadaren garin, rundunar soji ta kubutar da wasu daga cikin ‘yan matan.

A rahoton da muka samo daga jaridar Leadership, an ce jami’an sun ceto biyu daga cikin ‘yan matan sama da 200 da aka yi garkuwa dasu kuma aka yi musu auren dole tun shekarar 2014.

Wani rahoton sirri daga manyan majiyoyin tsaro, sun tabbatar da ceto ‘yan matan daga sansanin Gazuwa, wata hedikwatar kungiyar Boko Haram da aka fi sani da Gabchari, Mantari da Mallum Masari, mai tazarar kilomita tara zuwa garin Bama.

Makwannin da suka gabata ne rundunar sojin Najeriya ta ceto wasu ‘yan matan daban, kana suka ba da labarin cewa akwai sauran ‘yan mata sama da 20 da ke hannun ‘yan ta’addan har yanzu.

‘Yan matan makarantar ta Chibok biyu da sojoji suka ceto a baya kuma aka nuna su ga jama’a a kwanan baya su ne Mary Dauda da Hauwa Joseph.

Tserewar da suka yi daga sansanin ‘yan ta’addan ya faru ne, sakamakon gagarumin farmakin da dakarun Operation Hadin Kai suka ci gaba da yi wanda ya yi sanadin bullar yunwa da kauran dole a yankunan ‘yan ta’addan, inji Telegraph.

Idan za ku iya tunawa kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da dalibai mata 276, masu shekaru tsakanin 16 zuwa 18 a makarantar Sakandaren ’yan mata ta gwamnati da ke garin Chibok a ranar 14 ga Afrilu, 2014.

Sama da ‘yan matan makarantar 100 ne har yanzu ba a gansu ba ya zuwa ranar 14 ga Afrilu, 2021, shekaru takwas bayan da ‘yan ta’addan suka sace su.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here