Rundunar Sojin Najeriya ta Gano Daya Daga Cikin ‘Yan Matan Chibok da Boko Haram Suka Sace
Rundunar sojin Najeriya ta sanar da cewa, ta gano wata mata da ke garari a wani yankin Borno, wacce ‘yan Boko Haram suka sace.
Rahoton soji ya ce ana kyautata zaton matar na daga cikin ‘yan matan Chibok da aka sace a shekarar 2014.
Hakazalika, an gano ta ne tare da yaro, kana ana ci gaba da bincike don gano asalin tsuhen batan ta.
Read Also:
Borno- Dakarun runduna ta 26 Task Force Brigade, a ranar Talata, sun gano wata Mary Ngoshe, wacce a cewar rundunar sojin Najeriya, tana daya daga cikin ‘yan matan da aka yi garkuwa da su a makarantar Sakandaren ’yan mata ta gwamnati da ke Chibok a shekarar 2014.
Ngoshe, wadda aka same ta da wani yaro da ake kyautata zaton nata ne, sojojin sun tare ta ne a lokacin da suke sintiri a kewayen Ngoshe a jihar Borno.
Hakan na kunshe ne a wani sako da rundunar ya wallafa a shafin Twitter a safiyar Laraba.
Sakon ya ce:
“Dakarun 26 Task Force Brigade da ke sintiri a kewayen Ngoshe a jihar Borno a ranar 14 ga watan Yuni 2022 sun gano wata mata Mary Ngoshe da danta. Ana kyautata zaton tana daya daga cikin ‘yan matan da aka sace daga GGSS Chibok a 2014.Ana ci gaba da bincikarta.”