Harin Soji ya Kashe Mutane 23 a Sudan
Harin rundunar sojin Sudan ya kashe mutane aƙalla 23 da kuma raunata wasu fiye da 40 a kudancin birnin Khartoum.
An kai harin ne a kan babban sansanin mayaƙan RSF a kudancin Khartoum, amma ya kuskure, inda ya faɗa a kan wata babbar kasuwa da ke kusa da gidajen mutane.
Read Also:
Mutanen da hari ya ritsa da su sun haɗa da masy shaguna da kuma abokan cinikin su.
Ƙiyasin Majalisar Dinkin Duniya ya ce yaƙin da RSF ke yi da sojin Sudan a tsawon wata 18 ya yi sanadiyyar kisan mutane fiye da 150,000 da kuma raba wasu da dama.
Rahotanni sun ce yawan waɗanda suka samu rauni ya zarce wanda asibitoci a yankin za su iya kula da su.
Tun daga ranar Juma’a faɗa ya ƙazance tsakanin RSF da sojin Sudan, a yankin da mayaƙan na RSF suke da ƙarfin iko sosai.