Sojoji sun Cafke Mata Masu Haɗa Baki da ƴan Bindiga a Kaduna
Jihar Kaduna – Dakarun sojoji sun kama wasu mata guda biyu da ake zargin masu ba ƴan bindiga bayanai ne a jihar Kaduna.
Sojojin sun cafke matan ne da ake zargin suna haɗa baki da ƴan bindiga a ƙauyen SCC da ke ƙaramar hukumar Kachia ta jihar Kaduna.
Jaridar Daily Trust ta ce wani shugaban al’umma da ya so a sakaya sunansa ya bayyana hakan ga wakilinta ta wayar tarho a ranar Lahadi.
Sojoji sun cafke masu haɗa baki da ƴan bindiga
Read Also:
Ya ce sojoji daga Katari sun bi sawun waɗanda ake zargin ne a ranar Laraba bayan bayanan sirri da suka samu cewa sun je kasuwar ƙauyen SCC domin siyo kayan abinci da sauran kayayyaki ga ƴan bindigan.
Shugaban al’ummar ya ce tun da farko ƴan banga sun yi yunƙurin cafke waɗanda ake zargin sati biyu da suka wuce a kasuwar Kagarko amma sai suka tsere.
Wani ɗan banga a yankin, mai suna Shehu, ya tabbatar da kamun da aka yi wa waɗanda ake zargin. “Eh, sojoji ne suka kama matan guda biyu a ƙasuwar ƙauyen SCC ranar Laraba.”
– Shehu
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, ASP Hassan Mansur, bai ce uffan ba kan lamarin.