Sojojin Najeriya Sun Ceto Mutane 6 da Kai Garkuwa da su
Rundunar sojin Najeriya ta ceto wasu mutum shida da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a Kangon Kadi dake Chikun.
Wannan na zuwa ne kasa da sa’o’i 48 bayan da sojojin suka halaka ‘yan bindiga da suka kai farmaki NDA da FCE a Kaduna.
An ceto mutane shidan ne bayan ‘yan bindigan sun hangi sojoji sannan suka arce tare da barin wadanda suka yi garkuwa da su.
Kaduna – Kasa da sa’o’i 48 bayan halaka wadanda suka shirya karantsayen tsaro a Makarantar Horar da Hafsoshin Soji ta Kaduna da satar daliban kwalejin gandun daji, dakarun sojin Najeriya sun ceto wasu mutum shida a yankin Kangon Kadi dake karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.
Read Also:
Kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar ranar Litinin, The Nation ta rahoto.
Aruwan yace kamar yadda dakarun suka bayyana karkashin Operation Forest Sanity, sun je aikin kakkabe daji daga Damba zuwa Kangon Kadi kuma tarar da wurin wasu ‘yan bindiga a kusa da Kangon Kadi, Labi da kogin Udawa, jaridar Premium Times ta rahoto.
Kamar yadda yace:
“Yan bindiga sun tsere daga yankin Kangon Kadi sakamakon ruwan wuta da dakarun suka sakar musu inda suka bar mutum shida da suka yi garkuwa da su.
“Wadanda aka ceto sun hada da Iliya Gide, Rabi Ali, Hussaina Gide, Naomi Nuhu da diyarta Pamela Barage.
“Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya amshi rahoton tare da godiya inda ya yabawa dakarun kan yadda suka dage wurin ganin karshen ta’addanci.
“Za a bayyana wa jama’a duk wani cigaba da ake samu.”