Sojoji Sun Dakile Shirin ‘Yan Ta’adda Kan Lalata Muhimman Kadarorin Najeriya

 

Hedikwatar tsaro (DHQ) ta ce dakarun sojojinta sun dakile shirin da ‘yan ta’adda ke yi na lalata muhimman kadarorin kasar nan.

DHQ ta ce dakarun da ke kula da wadandan muhimman kadarorin suna aiki ba dare ba rana domin dakile duk wani shirin ta’addanci.

Rundunar sojin ta sanar da hakan ne ta bakin daraktan yada labarai na tsaro, Manjo Janar Edward Buba a taron manema labarai.

Sojoji sun dakile wani shirin kai farmaki

Buba ya ce tuni sojoji da hukumomin tsaro da ke da alhakin kare muhimman kadarorin kasar sun dauki matakan dakile hare-haren, in ji rahoton Vanguard.

Manjo Janar Buba ya ce:

“Muna sane da wasu shirye-shirye na ‘yan ta’adda na kaiwa wasu muhimman kadarorin kasar nan hari. Saboda haka, mun samar da matakan dakile irin wadannan hare-haren”

Buba ya yi kira ga ‘yan kasar da su marawa sojoji baya a yakin da suke da ‘yan ta’adda ta hanyar fallasa masu yin aiki da ‘yan ta’addan da ke zaune a cikinsu.

“Dole mu yaki ‘yan ta’adda” – Sojoji

Jaridar The Nation ta ruwaito daraktan yada labarai na hedikwatar tsaron ya ce wadannan ‘yan ta’addan makiyan Najeriya ne da ya kamata a yake su ta kowacce hanya.

Ya ce kusan kullum sai sojoji sun yi artabu da ‘yan ta’adda wadanda kullum suke kokarin kashe ‘yan kasar ko suka riga da suka yi kisan.

“A wannan fadan, akwai bukatar ‘yan kasa su fahimci cewa, ba za mu taba yin kasa a gwiwa ba a kan tsaro, idan kuwa muka nuna sarewa, to za matsalar tsaron za ta shafi kowa.”

– A cewar Manjo Janar Buba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here