Rundunar Soji ta Halaka Wasu ‘Yan Ta’adda, ta Rasa Wasu zakakurarun sojojinta Daga Ciki

Sojoji na cigaba da ragargazar ‘yan Boko Haram a jihar Borno, duk da ‘yan ta’addan na nemo sababbin dabarun kai wa sojojin hari

A ranar Litinin ne gumurzu ya turnike tsakanin ‘yan Boko Haram da sojoji da ke Damboa, bayan sun kai wa sojojin hari

Sakamakon karon battan, sun samu nasarar kashe ‘yan Boko Haram 22, yayin da sojoji 5 suka rasa rayukansu, 2 kuma sukaji raunuka ‘Yan kungiyar Boko Haram 22 ne suka mutu, yayin da sojoji 5 suka rasa rayukansu sakamakon wani gumurzu daya turnike tsakanin Sojoji da ‘yan ta’addan.

Wata majiya tace ‘yan Boko Haram din sun kai wa sojojin da ke Damboa hari a ranar Litinin. Sojojin sun ragargajesu na tsawon awanni 5. Sakamakon haka ne sojoji 5 suka rasa rayukansu, 2 kuma suka samu raunuka. Yan ta’addan sun sace wata motar sojojin, The Cable ta ruwaito.

Wata majiya ta daban ta ce, “Gumurzu ya turnuke tsakanin sojojin Operation Lafiya Dole da ‘yan Boko Haram, wanda sojoji suka yi kaca-kaca da su.” Duk da dai Kakakin rundunar, Sagir Musa, baya nan balle a ji ta bakinsa dangane da harin.

Dama sojoji 7 sun rasa rayukansu a ranar Alhamis. Rundunar na cigaba da kewaye wurin da ‘yan ta’addan suka kai musu hari, bayan sun saka kayan sojoji.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here