LABARI DA DUMI-DUMINSA: Dakarun Sojoji Sun Halaka Wasu Daga cikin ‘Yan Boko Haram a Borno
Rundunar sojoji ta Operation Lafiya Dole, ta samu nasarar kashe ‘yan Boko Haram 13 tsakanin 22 ga watan Oktoba zuwa 29, da kuma kwace makamai a hannunsu.
Kakakin rundunar sojin, John Enenche, ya sanar da hakan a ranar Juma’a yayin da yake bayar da jawabin sati a kan harkar tsaron arewa maso gabas a Abuja – Ya sanar da nasarar da rundunar suka yi ta mayar da harin da ‘yan Boko suka kai Mallam Fatori, Ngwuri Gana da Jamacheri da ke Borno Hedkwatar tsaro tace rundunar Operation Lafiya Dole ta ragargaji ‘yan Boko Haram 13 tsakanin 22 ga watan Oktoba zuwa 29, Daily Nigerian ta wallafa.
Read Also:
Kakakin rundunar, John Enenche ya sanar da hakan ranar Juma’a, yayin da yake bayar da jawabi karshen mako a Abuja a kan arewa maso gabas. Enenche ya ce sojojin rundunar OPLD na sama da kasa sun yi ayyuka da dama a cikin makonnan.
Ya ce rundunar ta kai wa ‘yan bindigan hari a maboyarsu, sun kuma mayar da harin da ‘yan bindigan suka kai musu sannan sun samar da tsaro ga ‘yan gudun hijira. A cewarsa, jagoran rundunar ya samu nasarar ragargazar ‘yan ta’adda da dama, sannan sun samu nasarar kashe sauran ‘yan ta’addan guda 13 a garin Mallam Fatori, Ngwuri Gana da Jumacheri da ke Borno.
Sun kuma samu nasarar kwace wasu abubuwa masu fashewa, IEDS da bindigogi 2 daga hannun ‘yan ta’addan. Rundunar ta samu nasarar mayar da hari 3 da ‘yan Boko Haram suka kai musu a Magumeri, Gajiram da Damboa da ke Borno. Ya kara da cewa, “A wannan karon battan, rundunar ta samu nasarar kashe ‘yan Boko Haram 13 da kwace miyagun makamai daga hannunsu. Gabadaya ‘yan ta’adda 22 kenan aka kashe a Damboa.”