Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Bindiga a Zamfara Tare da Kwato AK-47 Gudu 2
Rahoton da muke samu ya bayyana yadda sojojin Najeriya suka yi nasarar fatattakar ‘yan ta’adda a jihar Zamfara.
An hallaka ‘yan bindiga bakwai tare da kwato kayayyakin aikata barna masu yawa a hannun masu tada hankalin jama’a.
Hakazalika, an kama wasu ‘yan bindiga tare da kamo wanda kasurgumin da ke kai musu bayanan sirri game da jama’ar gari.
Jihar Zamfara – Rundunar sojin Najeriya karkashin tawagar Operation Hadarin Daji sun yi fata-fata da ‘yan bindiga bakwai tare da lalata mafakarsu da yawa da kuma kwace babura bakwai a karamar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara.
Wannan bayani na kunshe ne a cikin wata sanarwar da daraktan yada labarai na hedkwatar tsaron Najeriya da ke Abuja, Manjo Janar Musa Danmadami, rahoton Punch.
Read Also:
Danmadami ya ce, jami’an tsaron sun kuma kwato mujallun AK-47 guda biyu da kuma na’urar sadarwa ta Baofeng.
An kama ‘yan ta’adda bayan sheke wasu
A cewar wani yanki na sanarwar kamar yadda Daily Post ta tattaro.
“Biyo bayan kama wani mai kai wa ‘yan ta’adda bayanan sirri a ranar 21 ga watan Afrilu, jami’ai sun yi aikin bin kafa tare da kama ‘yan ta’adda biyu a ranar 22 ga watan Maris a garin Shinkafi da ke karamar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara.
“Kayayyakin da aka kwato daga wadanda ake zargin sun hada da babur daya da wayoyin hannu guda uku.”
“Babban kwamandan soji ya yada da kokarin jami’an Operation HADARIN DAJI kana ya karfafa gwiwar al’umma da su ci gaba da ba jami’ai bayanai masu muhimmanci akan lokaci game da ayyukan ‘yan ta’adda.”
Jami’an tsaro na ci gaba da samun nasara kan ‘yan ta’adda a bangarori daban-daban na Najeriya a irin wannan lokacin.