Hatsarin Jirgin Ruwa ya yi Sanadin Mutuwar Mutane 5 a Jihar Kano

 

Mutane a Jihar Kano sun shiga jimamin rashin yan uwansu da suka rasu sakamakon wani hadarin jirgin ruwa da ya faru a ranar Lahadi 23 ga watan Afrilu.

Kamar yadda hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar, an rasa rayyuka guda 5 sannan an ceto fasinjoji shida daga cikin jirgin ruwan bayan afkuwar lamarin a karamar hukumar Madobi.

Alhaji Saminu Abdullahi, jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta Kano ya ce an fara bincike kan afkuwar hadarin jirgin ruwan kuma za a sanar da sakamakon binciken daga bisani.

Jihar Kano – Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano a ranar Lahadi ta tabbatar da mutuwar wasu mutane biyar yayin da mutane shida suka tsira sakamakon hadarin jirgin ruwa a Dam din Kanwa da ke karamar hukumar Madobi na jihar.

Mai magana da yawun hukumar, Alhaji Saminu Abdullahi, ya fada wa Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa a wayar tarho a Kano cewa wani Umar Faruk-Dalada, ya kai musu rahoton afkuwar lamarin da inda ya faru, The Punch ta rahoto.

Ya ce:

“Lamarin ya faru a ranar 22 ga watan Afrilu, misalin karfe 5.40 na yamma.”

“Akwai kimanin mutane 11 a cikin jirgin ruwan, an ceto shida da ransu yayin da guda biyar an ceto su ba su numfashi.”

a lissafa sunayen wadanda suka rasa rayyukansu kamar haka:

Abdulrazak Nabara dan shekara 40

Dalha Muktar-Atamma dan shekara 40

Mustapha Ibrahim, dan shekara 45

Umar Isah dan shekara 35, da Umar Idris dan shekara 35.

Mai magana da yawun hukumar ya ce wadanda abin ya ritsa da su sun fito ne daga karamar hukumar Fagge na jihar, Daily Trust ta rahoto.

Ya ce an fara bincike dangane da hatsarin jirgin ruwan kuma za a sanar da rahoton abin da aka gano bayan an kammala binciken.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here