Motar da Ake Kira da Waya ta zo Har Inda Ake so ta Jawo Cece-Kuce a Kafar Sada Zumunta

Wani matashin da ya kira motarsa ta hanyar amfani da wayarsa sannan ta zo ya yadu a kafar sada zumunta ta Instagram.

A bidiyon, an ga lokacin da matashin ke kiran motar kan ta zo wurinsa ba tare da matuki ko wata matsala ba.

An kuma ga lokacin da motar ta zo daga wani tazara kana ta tsaya a kusa da matashin, lamarin da ya jawo cece-kuce.

Wani matashin da ya mallaki mota mai ban al’ajabi da ke sarrafa kanta ya nuna yadda motar ke aiki ba tare da matsala ba.

A bidiyon da ya yada, matashin ya latsa wasu ‘yan maballai a wayarsa, sai kawai motar ta fara zuwa wurinsa, ta kuma tsaya a inda yace ta tsaya.

Hakazalika, matashin ya yi murmushi tare da bayyana yadda fasahar zamani ke kara daukar hankali a wannan karnin na 21.

A cewarsa, a 2023 motoci za su iya zuwa ga masu su wanda kuma hakan abu ne mai daukar hankali da ke nuna kwarewa wajen fikirai fasihai.

Da yawan jama’a a kafar sada zumunta da suka bidiyon sun ce, za su so mallakar irin wannan mota, sun roki Allah ya taba su da talauci.

Martanin jama’a

@anniesxclusive:

“Allah ya raba ni da iyalai na dandana talauci amin.”

@hairmonybeautyclinic:

“Duk wannan bashi da wani tasiri a kiyama.”

@johnbull3140:

“Allah ya raba ni da talauci a rayuwata.”

@umalistifanus:

“Kai Allah ya raba ni da talauci.”

@nasty_perry_:

“@teslamotors za su mamaye duniya nan kusa.”

@offeciallauretta:

“A rayuwar nan kawai ka tara kudi.”

@karaokewithknaci:

“Bari na samu meye zan ci tukuna.”

@ifeanyigodson:

“Ba zan kara zuwa ga mota ba har abada.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here