Sojoji a Iran Sun Harba Hayaki Mai sa Hawaye Domin Tarwatsa Masu Zanga-Zanga
Kafofin yaɗa labaran Iran sun ce sojoji sun harba hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa masu zanga-zanga a wurare daban-daban da ke sassan ƙasar.
Duk da toshe kafofin intanet da hukumomi suka yi, hotunan bidiyo na ci gaba da ɓulla na gangamin.
Read Also:
Wani ganau ya ce: “ban taba ganin dalibai mata sun fita suna zanga-zanga ba, suna tattaki suna kuma kiran gwamnati ta sauka.”
Bidiyon sun nuna hotunan ɗaruruwan ɗalibai ƴan mata da suka bi sahun masiu gangamin.
An soma zanga-zangar tun watan da ya gabata sakamakon mutuwar wata mata da ta mutu a hannun hukumomin Hisba na ƙasar.
Wata ƙungiyar kare haƙƙin bil adama da ke Norway ta ce kusan mutum dari biyu ne suka mutu zuwa yanzu. Jami’an Iran sun ce sojoji aƙalla ɗari biyu suma sun mutu.