Bayan Kisan Zabarmari: Dakarun Sojoji Sun Kaiwa Manyan Boko Haram Hari

Hedkwatar tsaro ta sanar da yan Najeriya labari mai dadi bayan kisan Zabarmari da yan ta’adda suka yi a Borno.

Bisa rahoton hedkwatar tsaron a ranar Talata, 1 ga watan Disamba, dakarun soji sun lalata mafakar shugabannin Boko Haram a dajin Sambisa.

Kakakinta, Manjo Janar John Enenche ne ya bayyana hakan a ranar Talata.

Rundunar sojojin Najeriya ta dauki mataki kan yan ta’adda a Borno yan kwanaki bayan sun yi wa bayin Allah kisan kiyashi a jihar.

A cewar hedkwatar tsaro a ranar Talata, 1 ga watan Disamba, dakarun sojin Operation Lafiya Dole sun lalata mafakar shugabannin Boko Haram a dajin Sambisa.

A yayin aikinsu, rundunar sojin saman sun kuma kashe mayakan kungiyar da dama a Yale da ke jihar.

Rundunar a cikin wata sanarwa daga jagoran labarai na ayyukan tsarom Manjo Janar John Enenche, ta ce:

“A ci gaban aikin da sojin sama ke aiwatarwa na Operation Wutar Tabki 2, dakarun sojin sama na Operation Lafiya Dole sun lalata wasu mafakar shugabannin kungiyar yan ta’addan Boko Haram sannan sun kashe mayakansu da dama a wasu hare-hare mabanbanta a dajin Sambisa da kuma gabashin Yale, duk a jihar Borno.

“An kai hare-haren saman ne a jiya, 30 ga watan Nuwamba 202, bayan samun bayanai na sirri sannan wasu bincike sun nuna cewa wasu yan Boko Haram da suka aiwatar da hare-haren bayan nan kan bayin Allah sun nemi mafaka a dajin Sambisa yayinda aka gano sauran a yankin gabashin Yale.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here