Rundunar Sojoji Sun Kama Hadimin Gwamna Mai Daukar Nauyin ‘Yan Bindiga a Kudancin Najeriya
Rundunar sojoji ta bankado wanda yake da hannu dumu-dumu a daukar dawainiyar ‘yan bindiga a yankin kudancin Najeriya.
An gano wani hadimin gwamna, Tochukwu Okeke alias Owo a matsayin mai daukar nauyin ‘Unknown Gunmen’ a kudanci.
Okeke yana da kungiya wadanda suke amfani da makaman kare dangi wurin kai wa ‘yan sanda, sojoji da fararen hula farmaki.
Kudancin Najeriya – Rundunar sojin Najeriya sun samu nasarar damko hadimin gwamna ne wanda yake kulle-kullen rura wutar ta’addanci a kudu maso gabas.
An bankado wanda ake zargin yana da hannu akan kaiwa mutanen gari da jami’an tsaro farmaki a kudu maso gabacin Najeriya.
Hadimin gwamna ke daukar nauyin ‘Unkwown Gunmen’
Read Also:
PRNigeria ta tattaro bayanai akan yadda wani Tochukwu Okeke alias Owo, hadimin gwamna a kudu maso gabas ya daurewa ‘yan bindiga gindi kamar yadda rundunar division 82 na sojojin Najeriya a Enugu suka bankado.
Majiyar ta sojoji ta bayyana hakan ne inda ta bukaci a boye ta, tace hadimin yana da kungiya mai makaman kare dangi kuma suna kai hari ga ‘yan sanda, sojoji da fararen hula.
Kafin a kama wasu daga cikin shugabannin su a kuma lalata sansaninsu cikin ‘yan kwanakin nan, sun kaiwa ‘yan sanda da sojoji farmaki a Enugu ciki har da ofishin ‘yan sanda na Adani, wata matsayar sojoji dake kan titin Adani-Omoh, ofishin ‘yan sanda na Ezeagu, sansanin sojoji dake titin Orji River-Udi da wata dake kan titin Enugu Abakaliki.
Kungiyar ‘yan ta’addan wacce aka fi sani da “mugaye marasa imani” suna satar makamai a wurin jami’an tsaron da suke kaiwa farmaki.
Majiyar ta sanar da PRNigeria cewa an ragargaji daya daga cikin sansanayensu dake Akpawfu-Amangwunze dake karamar hukumar Nkanu ta yamma inda aka kwato makamai da dama da ababen hawa.