Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa da Mutane, Sun Kwato Makamai a Jihar Taraba

 

Jihar Taraba – Dakarun sojoji na ‘Operation Whirl Stroke’ sun cafke wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a ƙaramar hukumar Karim Lamido ta jihar Taraba.

Sojojin sun cafke mutanen ne tare ƙwato bindiga ƙirar AK-47 da alburusai a wani samame da suka kai a ranar, 16 ga watan Satumban 2024.

Sojoji sun cafke miyagu a Taraba

Tashar Channels tv ta rahoto cewa muƙaddaashin mataimakin daraktan yaɗa labarai na rundunar, Kyaftin Olubodunde Oni, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa.

Mutanen dai an daɗe ana nemansu kan zargin aikata laifuffuka da suka haɗa da fashi da makami, garkuwa da mutane da sayar da makamai.

Yadda aka cafke waɗanda ake zargin

Sanarwar ta bayyana cewa an cafke ɗaya daga cikinsu mai suna Ali Tambaya a ƙauyen Wanzani ɗauke da bindiga ƙirar AK-47 da alburusai 42 masu ƙaurin 7.62mm.

A yayin da ake bincike ya amsa cewa ya siyo bindigar ne daga wajen wani Alhaji Dandi kan kuɗi N500,000 kusan shekara biyar da suka wuce sannan ya siyo alburusan kan kuɗi N1000 kowannensu.

Ya kuma bayyana cewa wani mutum mai suna Alhaji Kiwo ne ya ba shi alburusai 38 daga cikin guda 42 ɗin domin ya ajiye masa.

Daga nan sai dakarun sojojin suka bi sauran waɗanda ake zargin inda suka cafke Alhaji Dandi yayin da suke ci gaba da ƙoƙarin cafke Alhaji Kiwo.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here