Rundunar Sojojin Najeriya ta Kama ‘Yan IPOB da Suka Kashe Jami’an ‘Yan Sanda a Akwa Ibom
Rundunar sojojin Nigeria ta ce ta kama wasu yan IPOB da ke da hannu wurin kaiwa jami’an tsaro hari a Akwa Ibom.
Bernard Onyeuko, mukadashin kakakin soja ya ce bayannan sirri ya nuna wadanda aka kama na da hannu a kisa da kona yan sanda.
Onyeuko ya bayyana hakan ne yayin da ya ke yi wa yan jarida bayanin nasarorin da rundunar ta samu a watannin Mayu da farkon Yuni .
Hedkwatar Tsaro ta Sojojin Nigeria ta ce an kama wasu daga cikin mambobin kungiyar Indigenous Peoples of Biafra (IPOB) ‘da ke da hannu wurin kisa da kona yan sanda a Akwa Ibom, The Cable ta ruwaito.
Akwa Ibom na daya daga cikin jahohin kudancin Nigeria inda ake kaiwa jami’an tsaro a watannin baya-bayan nan.
Read Also:
Hare-haren sunyi sanadin salwantar rayyukan jami’an tsaro 11 a cikin watanni uku da suka gabata.
A cikin sanarwar da ya fitar a ranar Alhamis, Bernard Onyeuko, mukadashin direktan, sashin watsa labarai na sojoji, ya ce sojoji sun fara yi wa miyagun dauki dai-dai.
Ya sanar da hakan ne yayin da ya ke yi wa manema labarai jawabi kan ayyukan rundunar daga ranar 20 ga watan Mayu zuwa 2 ga watan Yuni.
Onyeuko ya ce, “bayyanan sirri masu inganci sun bawa sojoji damar kamo mambobin IPOB/ESN” wadanda aka ce sune suke kai wa jami’an tsaro hare-hare a jahar.
“Sojoji a Ikot Ekpene sun kama wasu mambobin IPOB/ESN a karamar hukumar Essien Udim a Akwa Ibom bayan samun bayannan sirri kan ayyukansu a yankin,” in ji kakakin na sojoji.
“Wadanda ake zargin suna daga cikin mambobin IPOB/ESN da ke da hannu wurin kisa da kona yan sanda da ofisoshin yan sanda a yankin.”