Sojojin Najeriya Sun Kama Wani Mai Kaiwa ‘Yan Bindiga Rahoto, Sun Kuma Ceto Wasu

Dakarun Sojin Najeriya sun samun nasarar ceto mata da yaran da akayi garkuwa da su a jihar Katsina yayinda suka kwato shanu 75 da yan bindiga suka sace.

Diraktan yada labaran hedkwatar tsaro, Manjo Janar John Enenche, ya bayyana cewa daga cikin wadanda aka ceto akwai mata 18 da yara 5.

Hakazalika, ya bayyana cewa an damke wani mai kaiwa yan bindinga bayanai da wasu makamai.

A cewarsa, tuni an mayar da mutanen wajen iyalansu yayinda aka mayarwa masu shanu abinsu.

Enenche yace: “Dakarun Operation HADARIN DAJI na cigaba da kokari domin kare rayukan mutane na dukiyoyinsu a yankin arewa maso tsakiyan kasa.

“A ranar 29 ga Disamba, 2020, Sojoji sun yi arangama da yan bindigan da sukayi garkuwa da mutane kuma suka sace shanu a kauyen Kwayawa dake karamar hukumar Safana.

“Bayan ruwan wutan sama da jirgin Soji yayi kan yan bindiga, sun gudu sun bar mutanen da suka sace.”

“Sakamakon haka Sojoji suka ceto mata 18, yara 5 da kuma shanu 75 da aka sace.”

“A lokacin aka dame wani mai kaiwa yan bindiga bayani, Mohammed Saleh, da wasu makamaki.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here