Rundunar Sojoji Tayi Nasarar Kashe ‘Yan Ta’adda Tare da Kwace Makamansu
Rundunar sojoji ta Operation Whirl Stroke tana samun nasarar ragargazar ‘yan ta’adda.
A ranar Lahadi, 6 ga watan Disamban 2020, sun kashe ‘yan ta’adda 3 tare da kwace makamansu.
Hakan ya faru ne a kauyen Tsehombe-Adaka bayan ‘yan sa kai sun sanar da sojoji inda ‘yan ta’addan suke.
Read Also:
A jiya, ranar 6 ga watan Disamba ne rundunar Operation Whirl Stroke ta amsa kiran ‘yan sa kai a kan wani hari da ake zargin wasu makiyaya na kauyen Tsehombe-Adaka suka kai.
Take a nan aka yi karon batta tsakanin ‘yan ta’addan masu miyagun makamai da kuma jaruman sojojin.
Rundunar ta samu nasarar amsar bindiga kirar AK-47 da magazine daya mai rounds 5 ta 7.62mm Special ammunition.
Rundunar ta cigaba da yin sintiri don gudun kada ‘yan ta’adda su mamayesu, sannan a shirye take da su ga sun ragargaji duk wani dan ta’adda da zai kai wa yankin farmaki.
Mutanen yankin sun roki sojojin da su cigaba da ayyukansu, sannan sun lashi takobin sanar da su duk wani labari da suka samu a kan ‘yan ta’addan.