Sojoji Sun Kuɓutar da Matafiya 15 Daga Hannun ‘Yan Bindiga a Jahar Kaduna
Sojojin Operation Safe Haven sun kuɓutar da wasu matafiya 15 daga hannun yan bindiga a jahar Kaduna.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jahar, Samuel Aruwan, shine ya bayyana haka.
Yace dakarun sun kai ɗauki garin Jagindi, karamar hukumar Jema’a bayan an sanar da su abinda ke wakana.
Kaduna – Dakarun sojojin Operation Safe Haven sun kubutar da wasu matafiya 15 da yan bindiga suka sace a Jagindi, karamar hukumar Jema’a, jahar Kaduna ranar Lahadi, kamar yadda premium times ta rawaito.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jahar, Samuel Aruwan, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.
Yace sojojin sun kai ɗauki ne bayan wani kiran gaggawa da aka musu ƙan lamarin sace matafiyan.
Sojoji sun dakile harin yan bindiga
Aruwan yace:
“Dakarun sojin sun kai ɗauki inda suka fatattaki yan bindigan tare da kubutar da matafiya 15.”
Read Also:
“Maharan sun yi awon gaba da matafiya su 15 ne daga motoci biyu a yankin yayin da suke tsaka da tafiya.”
Kwamishinan ya bayyana sunayen mutanen da sojojin suka kuɓutar, da suka haɗa da, Maisaje Pam, Samuel Peter, Ziyau Abdul, Henry Dabo, Abduljabar Auwal, da Muhammad Ali.
Sauran sune; Dama Dabo, Ramatu Aminu, Muhammad Sani, Abdullahi Muhammad, Bashar Garba, Abubakar Musa, Saad Yakubu, Maryam Ibrahim, da kuma Lami Bitrus.
Gwamnatin Kaduna ta yaba da kwazon sojoji
A cewar Mista Aruwan, mukaddashin gwamnan jahar, kuma mataimakiyar gwamna, Hadiza Balarabe, ta jinjina wa sojojin bisa kai ɗauki cikin gaggawa.
Sojojin na cigaba da gudanar da Operation din bincike da kuma kubutar da mutane a yankin.
Duk da kokarin da jami’an tsaro suke na magance matsalar tsaron jahar Kaduna, yan bindiga na cigaba da cin karen su babu babbaka wajen watsa mutanen kauyuka, suna kashe wasu sannan su sace wasu.
Wasu na samun sa’ar kubuta daga hannun ɓarayin bayan an biya kuɗin fansa, wasu kuma suna cigaba da tsare su a daji na tsawon makwanni da watanni.