Sojoji Sun Mamaye Titunan Abuja Gabanin Zanga-Zanga a Najeriya

 

Direbobi a kan babbar hanyar Keffi zuwa Abuja a ranar Litinin sun shiga tsaka mai wuya bayan da sojoji suka tare babbar hanyar domin gudanar da bincike kan motocin da suka nufi Abuja, babban birnin Najeriya.

Sojojin sun dasa shingen bincike a barikin sojoji na Sani Abacha kafin shataletalen AYA.

Jami’an tsaro dai ba su bayar da wata sanarwa ba kafin toshe titin lamarin da ya janyo cunkoson ababen hawa har zuwa gadar Nyanya, sama da kilomita 12 daga wurin binciken motocin.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ma’aikata da masu tireda da ke aiki a Abuja, suna zaune a wajen tsakiyar birnin a wurare kamar Nyanya da Karu da Maraba da Masaka.

Bayan shafe tsawon sa’oi a wuri ɗaya – babu gaba, babu baya, akasarinsu daga bisani sun yanke shawarar komawa gida.

Wasu matasa a Najeriya na shirya zanga-zangar gama-gari daga 1 ga watan Agusta saboda tsadar rayuwa da taɓarɓarewar tattalin arziki a ƙasar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here