Sokoto: Sojoji Sun Tabbatar da Mutuwar Jami’ansu a Hannun Mayakan ISWAP a Yankin Sabon Birni

 

Rundunar sojojin Najeriya ta ce jami’an sun murkushe wani hari da mayakan ISWAP da ‘yan bindiga masu satar mutane suka kai a sansaninsu da ke kauyen Burkusuma na karamar hukumar Sabon Birni a Sokoto.

Wata sanarwa da kakakinta ya fitar, Benjamin Olufemi Sawyerr na cewa gungun mahara ne suka far musu da misalin 5:30 na safiyar Lahadi, bayan samun damar amfani da layin sadarwar Nijar wajen kitsa harin.

Yankin Sabon Birni na yawaita fuskantar barzanar hare-hare musamman a watanin baya-bayana daga ‘yan bindiga.

Sanarwar ta kuma ce duk da kokarin dakarun sojoji wajen murkushe maharan, an samu jami’anta da suka rasa rayukansu.

Akwai kuma mayakan da suka tsere zuwa cikin Nijar da yanzu haka ana kan farautarsu a samamen hadin-gwiwa tsakanin sojojin Najeriya da na Nijar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here