Rundunar Sojojin Najeriya Zata Iya Kawo Karshen Boko Haram – Ministan Tsaro
Ministan tsaro, Manjo janar Bashir Magashi, ya ce sojojin Najeriya sune mafi nagarta a cikin Afirka.
Magashi ya ce rundunar sojin Najeriya za ta iya kawo karshen Boko haram a arewa maso gabas.
Ya ce har kasashen ketare irin Sierra Leone suka je kuma suka yi samu nasarori masu yawa.
Ministan tsaro, Manjo janar Bashir Magashi, ya ce sojojin Najeriya suna daga cikin sojoji mafi nagarta a Afirka. Ya fadi hakan ne a ranar Alhamis, inda yace suna da damar kawo karshen duk wani makiyi idan aka ba su damar yin hakan.
Read Also:
A cewar Magashi, rundunar soji za ta iya kawo karshen Boko Haram a arewa maso gabas, saboda sun ci nasara a yakin da suka je cikin wasu kasashen ketare.
A cewarsa, “A Afirka, ya kamata sojojin Najeriya su zama na daya a kwazo, saboda mun dade muna samun nasarori har a kasashen ketare. Mun je ECOMOG, mun yi iyakar kokarinmu. Mun je Sierra Leone, mun ci nasara. Amma sakamakon dadewar wannan yakin, mutane har sun gaji.
“Yan Boko Haram ba sa tsayawa wuri daya, da zarar sun kai farmaki wani wuri sai su gudu su koma wani wurin. Matsalar kawai ba mu san inda suke zama bane. Yanzu kuwa da muka gano su, gashi nan rundunar sojin sama da ta kasa suna karar da su.”
Magashi ya fadi hakan ne a wata tattaunawa da gidan Talabijin na Channels sukayi dashi, wanda The Punch ta kula dashi yau.