Dakarun sojojin kasan Najeriya Sun Kashe ‘Yan Bindiga 48 da Kwamandojinsu 5 a Jahar Zamfara

 

Dakarun sojojin kasan Najeriya karkashin atisayen Operation Tsare Mutane sun sheke ‘yan bindiga 48 da kwamandojinsu 5.

Hakan ta faru ne a samamen da suka kai sansanonin ‘yan bindigan dake jahar Zamfara da jahohi masu makwabtaka da su.

Kwamandojin da aka halaka sun hada da Yellow Mai-Bille, Sani Meli, Dan- Katsina da Sama’ila Bakajin Bari.

A daren Lahadi ne rundunar sojojin Najeriya tace dakarun runduna ta 8 da aka tura yakar ‘yan bindiga da suka addabi Zamfara da jahohi dake da makwabtaka dasu sun kashe kwamandojin ‘yan bindiga 5 tare da wasu miyagu 48 bayan musayar wuta da aka yi.

Har ila yau, dakarun sun yi kokarin ceto mutum 18 da aka yi garkuwa dasu daga sansanin ‘yan bindigan, Vanguard ta ruwaito.

Birgediya janar Mohammed Yerima, daraktan hulda da jama’a na sojojin kasa, wanda ya sanar da hakan a wata takarda ya kara da cewa an tarwatsa sansanin ‘yan bindiga masu yawa inda aka samo miyagun makamai.

Ya ce, “Dakarun runduna ta 8 ta sojin kasa dake aiki a Zamfara da sauran jahohi sun samu manyan nasarori a yaki da ‘yan bindiga da suke yi.

“Rundunar tun farko ta kaddamar da sabon atisaye mai suna Operation Tsare Mutane bayan umarnin da suka samu daga shugaban sojin kasa, Laftanal Kanal Ibrahim Attahiru.

“Babban kwamandan rundunar, Manjo Janar Usman Yusuf ya kaddamar da atisayen wanda zai fara daga 23 ga watan Maris zuwa 2 ga watan Afirilun 2021 a karamar hukumar Maradun na jahar Zamfara.

“Cike da nasara dakarun suka tarwatsa sansanonin ‘yan bindigan dake Jaya, Kadaya da Bayan ruwa da sauransu. “Dakarun sun yi nasarar sheke ‘yan bindiga 48 yayin da shugaban ‘yan bindigan yankin, Jummo ya samu miyagun raunika a kafafunsa.

Dakarun sun ceci mutum 18 da ‘yan bindigan suke rike dasu. “An samo bindigogi kirar AK47 8 da wasu miyagun bindigogi hudu daga ‘yan bindgan.

“Kwamandojin ‘yan bindigan 5 da suka hada da Yellow Mai-Bille, Sani Meli, Dan- Katsina da Sama’ila Bakajin Bari duk sun sheka lahira yayin da Nasanda ya sha da kyar.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here