Sojojin Najeriya Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 6 a Samamen da Suka Kai Kasuwar ‘Yan Boko Haram

 

Sojojin Najeriya na runduna ta 21 sun ragargaji wata haramtacciyar kasuwar ƴan ta’addan Boko Haram da ke Bama a jihar Borno.

Masani kuma mai sharhi kan tsaro, Zagazola Makama, ya ce sojin sun kashe yan ta’adda Shida sun kama gomman su a samamen.

Rahoto ya nuna cewa ana kasuwancin Masara, Wake, Gishiri da sauran su da ƴan ta’addan a matsayin musaya da ƙarfe.

Borno – Rundunar soji ta 21 da ke sansani a Bama ta hallaka mayaƙan kungiyar yan ta’addanci Boko Haram yayin da suka kai samame wata kasuwa da yan ta’adda suka kafa ba bisa ƙa’ida ba a ƙaramar hukumar Bama, jihar Borno.

Daily Trust ta rahoto cewa Sojojin tare da haɗin guiwar yan Sa’kai na Civilian Joint Task Force (CJTF) sun kai samame kasuwar ne da misalin karfe 11:00 na safiyar ranar Laraba.

Bayanai sun nuna cewa jami’an tsaron cikin shiri suka mamaye Kasuwar wacce ake kira ‘Kasuwar Daula’ dake ƙauyen Bararam, a yankin Bama, suka buɗe wa tsagerun wuta.

A cewar Zagazola Makama, masani kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi, ana tsaka da gudanar da harkokin Kasuwanci lokacin da Sojoji suka danno suka tsarwatsa kasuwar.

Ya ce yayin da yan tada ƙayar bayan suka ga shigowar sojojin, nan take suka buɗe wuta amma jajirtattun sojojin suka maida martani aka yi ɗauki ba daɗi.

Ya ƙara da cewa Jami’an tsaro sun yi nasarar tura yan ta’adda Shida lahira kuma suka kame wasu da dama, sannan suka kwace makaman su.

Makama ya ce:

“Sun damƙe gomman mayaƙan Boko Haram da suka haɗa da masu samar musu da kayan aiki, masu haɗa kai da su, kana kuma suka kwato makamai da dama.”

Me ake yi a kasuwar?

Ratoto ya nuna cewa masu kasuwanci a wurin suna sayar da abubuwa kamar Masara, Wake, Gishiri Maggi, Tufafin da aka taɓa amfani da su, Kwayoyi da Man Fetur ga ƴan ta’adda domin musaya da ɗanyen ƙarfe.

Legit.ng Hausa ta gano cewa yanzu haka an kai waɗan da suka shiga hannu Hedkwatar Rundunar Amoured Brigade da ke garin Bama domin cigaba da bincike.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here