Yanda Sojojin Najeriya ke Samun Nasara Aka Kungiyar Boko Haram

 

Sojojin Najeriya suna cigaba da samun nasarar ragargazar ‘yan Boko Haram da suka yi garkuwa da wasu mutane 5 a Maiduguri.

‘Yan ta’addan sun nemi naira miliyan 2 daga hannun iyalansu, amma sai dai tarkonsu bai kama kurciya ba.

Sojojin sun ceto mutane 5 din, sun kuma kashe daya daga cikin ‘yan Boko Haram din, sauran kuma sun tsere da raunika.

Rundunar sojin Najeriya suna cigaba da samun nasarar ragargazar ‘yan Boko Haram a kauyakun waje-wajen babban birnin Borno, Maiduguri.

Mukaddashin jami’in hulda da jama’a na rundunar soji, birgediya janar Benard Onyeuko, yace runduna ta 251 ta bataliyar soji ta kaiwa wasu ‘yan Boko Haram farmaki a Molai, kamar yadda jaridar This Day ta ruwaito.

A cewarsa, sai da sojojin suka yi nazari kwarai, kuma suka yi amfani da dabara ta musamman, bayan iyalan wasu mutane da ‘yan ta’addan suka yi garkuwa da su sun bukaci Naira Miliyan 2 a hannunsu sun kai musu rahoto.

Kamar yadda takardar tazo: “Cikin kwarewa da dabara, rundunar sojin suka takura wa ‘yan Boko Haram a kan su dakata daga amsar kudi daga hannun mutanen.”

Ya ce sun fara ragargazar ‘yan Boko Haram din, har su ka kashe daya, sauran kuma suka gudu da ciwuka sakamakon harbin da suka sha.

Sojojin sun samu nasarar amso yaran guda 3, tare da mata 2 ba tare da wani abu ya samesu ba. Sannan sun samu bindiga AK47 da wani babur.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here