Harin NDA: Sunayen Sojojin da ‘Yan Bindiga Suka Kashe da  Sojan da Suka Sace

 

A ranar Talata da safe ne wasu miyagun mutane suka harbe wani babban soja mai suna Wulah da wani CM Okonkwo har lahira.

‘Yan bindigan sun afka har cikin barikin Afaka ta NDA da misalin 1am yayin da sojoji da dama suke ta bacci.

An samu rahotanni a kan yadda ‘yan bindigan suka yi garkuwa da wani Manjo Datong sannan suka ji wa wani daban miyagun raunika.

Kaduna – A ranar Talata da sassafe ne wasu ‘yan bindiga suka kai farmaki barikin Afaka dake NDA inda suka harbe wani soja mai mukamin Lieutenant Commander mai suna Wulah, da wani Flying Lieutenant CM Okoronwo har lahira.

Daily Trust ta ruwaito yadda ‘yan bindigan suka afka barikin da misalin karfe 1am.

Wata majiya daga barikin tace ana zargin wadanda suka kai farmakin sun bari ne daidai lokacin da mutane da dama suke bacci.

Majiyar ta ce, an kara tsananta tsaro don gudun ‘yan bindigan su tsere da wadanda suka yi garkuwa da su.

Daily Trust ta ruwaito yadda su ka yi garkuwa da wani Manjo Datong a ranar yayin da suka ji wa wani soja mai mukamin 2nd Lieutenant miyagun raunika sakamakon harbe-harben, yanzu haka yana asibitin NDA ana kulawa da lafiyarsa.

Bai wuci mako guda kenan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya hori shugabannin tsaro ba akan su kara dagewa wurin ganin sun kawo karshen rashin tsaro.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here