Matsalar Tsaro: A Sokoto Kawai Mun Taba Binne Mutane 76 a Rana Daya – Sarkin Musulmai

 

Sarkin Musulmi ya sake koka wa kan yadda ake fama da matsalar rashin tsaro.

Muhammad Sa’ad Abubakar III yace ba zai daina fadawa gwamnati gaskiya ba.

Sultan yace a magance matsalar ba tare da an neni taimakon kasashen waje ba.

Abuja – Mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III, yace ba a bada cikakken labari a kan irin kashe-kashen da ake fama da shi a yau.

Mutane ba su sanin abubuwan da ke faruwa Daily Trust ta rahoto Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar III yana cewa sha’anin rashin tsaro ya yi kamari, ya kuma yi alkawarin cigaba da fadin gaskiya.

Da yake jawabi a wajen taron majalisar addinai na kasa a birnin tarayya Abuja, Sultan ya bada labarin wata rana da aka binne mutum 76 a garin Sokoto.

“A Sokoto kurum, akwai wata rana da muka birne mutane 76, ‘yan ta’adda suka kashe su haka kurum, mutane ba su samu labarin wannan ba.”

“Akwai kuma ranar da muka binne gawar mutane 48 a Sokoton dai, amma ba a ji labarin ba.”

Mai alfarma Sarkin Musulmin ya bayyana cewa dole a bankado mutanen da suke yin wannan danyen aiki, domin a yanke masu hukuncin da ya dace.

A nemi gudumuwar kasashen waje?

Sa’ad Abubakar III ya yi kira ga jami’an tsaro su nemo duk masu daukar nauyin ta’addanci, ko da kuwa shugabannin addinai ne ko jagororin wata kabila ne.

“Dole mu dage wajen kawo karshen wannan lamarin, idan mun ga dama, za mu iya tsaida shi. Idan aka gayyaci kasar waje, ba a san yadda za ta kare ba.”

“Ina wannan bayani ne daga zuciya ta saboda mun damu da yadda abubuwa suke kasance wa.”

Jaridar ta rahoto Sultan yana zargin shugabannin al’umma da ‘yan siyasa da yin kalaman kiyayya da za su iya jawo a rika kashe mutane ba da dalili ba.

“Ba za ka kashe mutum bai ji ba, bai gani ba, da sunan addini, kuma ka ce za ka tafi gidan Aljanna, kana yaudarar kanka ne, wutar jahannama za ka shiga.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here