An Soma Shari’a Kan Kisan Gillar da Aka yi wa Tsohon Shugaban ƙasar Burkina Faso, Thomas Sankara
Yau ake soma shari’a kan kisan-gillar da aka yi wa Thomas Sankara.
A wannan Litinin ne za a buɗe wata shari’ah a birnin Ouagadougou kan yi wa tsohon shugaban ƙasar Burkina Faso Thomas Sankara kisan gilla.
An kashe shugaban mai rajin samun ‘yancin kai ne a wani juyin mulki cikin 1987.
Mutumin da ya gaje shi, Blaise Compaore, na ɗaya daga cikin mutanen da ake gurfanarwa a kotu – bayan ya jagoranci ƙasar tsawon sama da shekara ashirin kafin ya tsere zuwa neman mafaka a Aburi Kwas.
Ya sha musanta hannu a kisan gillar da aka yi wa Sankara.