Hukuncin da Ƴan sandan Somaliya Suka Dauka Kan Mata Masu Saka Niƙabi
Ƴan sanda a birnin Kismayo da ke kudancin Somaliya sun ce za su ɗaure ko su ci tarar matan da ke rufe fuskarsu da niƙabi saboda fargabar cewa mayaƙan Al-Shabab na iya yin shigar burtu wajen kai hare-hare.
Read Also:
Shugaban rundunar ƴan sanda ya ce jami’ansa sun ƙwace ɗaruruwan niƙabi cikin kwanaki huɗu da suka gabata.
An soma ƙaƙaba haramcin a 2021 sai dai galibi an yi watsi da shi.
Ranar Juma’a da daddare ne Al Shabab da ke da alaƙa da ƙungiyar al-Qaeda ta kai mummunan hari a Mogadishu babban birnin ƙasar. Mutum 37 ne suka mutu, fiye da ɗari biyu kuma suka ji rauni.
A baya-bayan nan ne sojojin Somaliya suka kashe gomman mayaƙa masu iƙirarin Jihadi a Jubaland a don haka akwai yiwuwar akai hare-haren ramuwar gayya.