Minsitan Harkokin Wajen Sudan ya Yaba wa Sojojin Kasar Kan Dakile Yunkurin Juyin Mulki

 

Ministan harkokin wajen Sudan ya yaba wa sojojin kasar kan yadda suka dakile yunkurin juyin mulki ranar Talata.

Yayin da take zantawa da BBC, Mariam El Sadiq Al Mahdi ta ce hakan ya nuna jajircewar sojojin son ganin dimokradiyya ta tabbata.

El Sadiq Al Mahdi ta ce wadanda suka yi yunkurin juyin mulkin magoya bayan tsohon shugaban kasar Omar Albashir ne.

Ta ce an gano yunkurin juyin mulkin ne lokacin da suka yi yunkurin kwace gidan rediyon Omdurman.

Ta kara da cewa zuwa yanzu babu wata alamar kutse daga waje.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here