Rundunar Sojin Sudan ta Zargi Habasha da Kashe Sojojinta 7
Rundunar sojin Sudan ta zargi sojojin kasa na Habasha da zartar da hukuncin kisa a kan sojojinta bakwai da kuma wani farar-hula da ke tsare a hannunta.
Zargin wanda ke kunshe a wata sanarwa da kafar yada labarai ta gwamnatin Sudan ta fitar bai yi wani karin bayani ba.
Sai dai ta bayyana matakin da cewa abu ne mai hadari, kuma za a mayar da martani a kai.
Read Also:
Zuwa yanzu babu wani martani da hukumomin Ethiopia suka yi game da zargin na Sudan.
A cikin shekara biyu da ta gabata, rikicin da kasashen biyu suka dade suna yi a kan iyaka ya kara zafafa, inda ake samun dauki-ba-dadi, daga lokaci zuwa lokaci a tsakaninsu a yankin al-Fashaga.
Daman Sudan tana jin haushin Habasha saboda katafariyar madatsar-ruwan da kasar ke ginawa a Kogin Nilu, wanda abu ne da take ganin zai rage mata ruwan da take samu.