Zanga-Zanga: Sudan ta Kudu ta Katse Layukan Intanet a Kasar
An katse layukan intanet a Sudan Ta Kudu da takaita samun layukan wayoyi yayin da mahukunta ke kokarin murkushe wani shirin zanga-zanga a fadin kasar kan adawa da shugabannin siyasa.
Read Also:
An tura karin jami’an tsaro birnin Juba.
Gamayyar kungiyoyin da suka shirya zanga-zangar ta zargi Shugaba Salva Kiir da mataimakinsa Riek Machar da gazawa tare da bukatar su yi murabus.
An kama masu fafutika da dama kan alaka da kungiyar a kwanakin baya-bayanan.