Apostle Suleman ya Ja Kunnan Masu Sukar Bishop Kukah

Ya zama dole a bayar da tabbaci da mutunta tsaron Mathew Kukah, a cewar Apostle Suleman.

Faston ya ce mutane su kyale limamin cocin na Katolika sannan su mayar da hankali kan yaki da rashin tsaro.

A cewarsa, Allah zai mayar da martani ga duk wanda ke shirin taba dansa.

Apostle Johnson Suleman, babban fasto kuma Shugaban cocin Omega Fire Ministries International, ya aika gagarumin gargadi ga wadanda ke sukar Bishop Mathew Kukah.

Limamin cocin ya bayyana cewa kada a kuskura ayi wani abu da zai illata limamin cocin na Katolika kan furucin da yayi a kan gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

“Kada wani abu ya samu Bishop Kukah. Wadanda ke shirya hakan sun san abunda nake fadi. Kada mu tunzura abun ya kara girmama. Ku kyale mai suka da zuciya daya dannan ku magance yan ta’adda. Kada ku taba Bishop Kukah idan kuka taba ministocin Allah, Allah zai mayar maku da martani.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here