Jerin Sunayen Jihohin Arewacin Najeriya 7 da za su Fuskanci Yunwa – Bankin Duniya

 

Y sassan duniya da matsalolin yunwa da za su fuskanta.

A sashen Afirka ta yamma da ta tsakiya, rahoton mai taken ‘Food Security Update 2024’, ya bayyana cewa wasu jihohi guda bakwai na arewa maso yammaci da gabashi da wadanda za su fuskanci matsalar yunwa tun daga farkon shekarar nan har zuwa watan Mayu.

Jihohin dai su ne:

Adamawa
Borno
Kaduna
Katsina
Sokoto
Yobe
Zamfara

Rahoton dai ya bayyana dalilan rashin tsaro na ‘yan bindiga da ke satar jama’a a jihohi kamar Kaduna da Katsina da Sokoto da Zamfara, inda su kuma Borno da Yobe da Adamawa ke fuskantar matsalar Boko Haram.

Harwayau, rahoton ya yi wa jihohin kudin goro da sauran sassan Najeriya da ke fama da matsalar tsadar rayuwa a matsayin daya daga cikin dalilan da zai sa jihohin su fuskanci yunwa.

Da ma dai bankin na duniya a wani rahoto ya ayyana Najeriya a matsayin kasa ta 6 a jerin kasashen da suka fi talauci.

Wadanne matakai za a bi domin rage radadin yunwa?

Masana na cewa matakan iri biyu ne wato na gajere da dogon zango:

Gajeren zango:

Dr Mohammed Sulaiman Kani masani kan tattalin arziki da samar da abinci kuma malami a kwalejin ilimi ta tarayya da ke Kano ya ce dole ne gwamnonin jihohin da abin ya shafa su bude rumbunan abinci na jihar su fito da kayan abinci a sayar a kan farashi mai rahusa.

Masanin ya kara da cewa “dole ne a yi kokarin samar da kwarkwaryar tsaro ga mutanen yankunan domin samun damar yin noma.”

Dogon zango:

Dangane kuma da matakai na dogon zango, masanin ya lissafa abubuwa guda hudu:

Tsaro
Noma
Samar da wutar lantarki
Tabbatar kamfanonin cikin gida sun tashi

“Idan dai har gwamnati ba za ta tabbatar da wadannan abubuwan ba to fa a rahoton bankin na duniya na nan gaba za a iya ganin sunayen wasu jihohin sabbi sun fado cikin yanayin yunwa da talauci,” in ji Dr Mohammed Kani.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com