Har Yanzu Ban Karbi Wata Takarda a Hukumance da ke Neman Kame Abba Kyari ba – Ofishin Ministan Shari’a

Ofishin ministan shari’a a Najeriya ya magantu kan tuhumar da Amurka ke yi wa Abba Kyari.

Wannan ya biyo bayan dakatar da Abba Kyari bisa zargin karbar cin hanci, wanda FBI ta yi

Ofishin ministan ya ce har yanzu bai karbi wata takarda a hukumance da ke neman kame Kyari ba.

Abuja – Ofishin Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, kuma ministan Shari’a Abubakar Malami, ta ce har yanzu ba ta karbi wata takarda a hukumance daga cibiyar binciken Amurka ta FBI ba da ke neman damar kame mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Abba Kyari.

Wannan ya fito ne daga bakin mataimaki na musamman ga ministan, Umar Gwandu yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da wakilin jaridar Punch.

FBI ta zargi Abba Kyari da karbar cin hanci daga hannun Hushpuppi, wani dan damfara dake fuskantar zaman kotu a Amurka, bayan kame masa wani abokin harkallarsa.

Duk da cewa Kyari ya karyata zargin, Hukumar Kula da Ayyukan ‘Yan Sanda ta fara bincike kan gaskiyar lamarin yayin da aka dakatar da Abba Kyari.

Lokacin da aka tambaye shi ko Ofishin AGF ya samu wata takarda daga FBI ko rundunar ‘yan sandan Najeriya dangane da sammacin kama Kyari, mai taimaka wa Malami ya ce ba a sanar da ofishin ba.

Ofishin AGF ne ke da alhakin batutuwan da suka shafi mikawa, maida mai laifi gida da canja wuri ga wadanda ake zargi ko wadanda ake nema.

Gwandu ya ce:

“Babu wata hanyar sadarwa a hukumance kan hakan.”

Mai taimaka wa AGF ya kuma ce ba za a fara tsarin mika Kyari ba har sai an samu bukatar hakan a rubuce daga Amurka.

Duk da haka, ya ba da tabbacin cewa:

“Komai za a yi shi bisa ga doka kuma bisa dogaro da manyan abubuwan da doka ta tanada”.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here