2023: Har Yanzu Talakawa za su yi wa Shugaba Buhari Mubaya’a Kuma ba za su Taba Yin Watsi da Shi ba – Fadar Shugaban Kasa ga PDP

Fadar shugaban kasa ta yi jawabi kan halin da zaben 2023 zai dauka, kasancewar talakawa na kaunar Buhari.

Fadar ta caccaki PDP bisa yi wa ‘yan Najeriya fatan karya kan mulkin APC musamman ta shugaba Buhari.

A ci gaba da shirin babban zaben 2023, ‘yan siyasa na ci gaba da jefo zantuka kan yadda za ta kaya Fadar Shugaban kasa a ranar Talata ta fada wa babbar jam’iyyar adawa ta PDP, da ta daina sa ran lashe babban zaben na 2023, saboda har yanzu talakawa za su yi wa Shugaba Muhammadu Buhari mubaya’a kuma ba za su taba yin watsi da shi ba.

An zargi PDP da ba ‘yan Najeriya fatan karya cewa saboda rashin tabuka abin a zo a gani a jam’iyyar APC, a matakin kasa, cewa (PDP) za ta karbi mulkin da ta rasa a hannun APC a shekarar 2023, Daily Nigerian.

Amma Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban kasa kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu, wanda ya yi magana jim kadan bayan Sallar Idi a Daura ta Katsina, ya ce ’yan Najeriya sun sani daram kuma ba za su yarda wani bangare ya karbi mulki a 2023 ba.

A cewarsa:

“Shugaban yana da goyon baya mara girgiza ba kawai a mahaifarsa ba har ma a duk fadin kasar kuma ya isa ga ‘yan adawa su yarda cewa Shugaban kasar yana da matukar muhimmanci ga jam’iyya mai mulki da ‘yan Najeriya baki daya.

“Har ilayau, ya zama musu cikas ga siyasa da ba za su iya wargazawa a zaben 2023 ba.

“Mun yi imanin cewa PDP da sauran jam’iyyun adawa suna bakin ciki da fatan karya kan mulki a zaben 2023.

“Talakawa ba za su taba yin watsi da shugabancin Shugaba Buhari da APC ba. Ina tabbatar muku da cewa a 2023, talakawa za su jira Shugaban kasa ya nuna hanya cikin ladabi da abi da ya gina wa kasa ta fuskar samar da ababen more rayuwa da kuma jin dadin matasa a kasar.

“Babu wanda zai dauki kasada ta hanyar gayyatar wani bangare ya zo ya karbi mulki a 2023.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here