‘Yan Taliban Sun Fafata da Masu Gadin Iyakar Iran

 

Kungiyar Taliban da ke mulkin Afganistan sun fafata da masu gadin kan iyakar Iran a kan iyakar ƙasashen biyu.

Mayakan sun ce an kashe daya daga cikinsu a fadan da aka yi a ranar Lahadi a kan iyakar da ke tsakanin lardin Nimroz na Afghanistan da Hirmand na Iran.

Kowace ƙasa ta ɗora wa ɗayar laifi akan lamarin, wanda shi ne fada na baya-bayan nan da aka yi tun bayan da kungiyar Taliban ta ƙwace iko da Afghanistan shekara daya da ta wuce.

A watan da ya gabata, Iran ta ba da rahoton mutuwar daya daga cikin masu gadinta a wani lamari da ya faru a wannan yanki.

Ba a san hakikanin yanayin fadan na baya-bayan nan ba, amma wani rahoton Iran ya ce an fara harbe-harbe ne a lokacin da kungiyar Taliban suka yi kokarin ɗaga tutarsu a yankunan da ba na Afghanistan ba.

Rahotanni sun ce ba a samu asarar rayuka ba a bangaren Iran.

Sai dai har kawo yanzu rundunar yan sanda bata fitar da sanarwa kan harin ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here