Tarihin Rayuwar Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana daya daga cikin manya-manyan ‘yan siyasan Najeriya.
Sannan Buhari yana daya daga cikin manya-manyan masu dukiyar Najeriya, ba zaka sani ba sai ka bincika.
Cikin wannan labarin akwai tarihin Buhari, dukiyar da ya tara, iyalinsa, karatunsa da komai na rayuwarsa.
Muhammadu Buhari babban dan siyasa ne a Najeriya, kuma yanzu haka shugaban kasa. Ya mulki Najeriya tsakanin 1983 zuwa 1985 a matsayinsa na soja.
An kuma zabe shi a matsayin shugaban kasa na mulkin farar hula a 2015, kuma ya zarce a 2019. Kafin zabensa, ya rike manyan makamai a kasar nan.
An haife shi a 17 ga watan Disamban 1942 a karamar hukumar Daura dake jahar Katsina. Yanzu haka, shekarunsa 78 da haihuwa. Iyayensa Fulani ne, mahaifinsa, Hardo Adamu, mahaifiyarsa kuma Zulaihat.
Buhari ya fara karatunsa ne a Mai’adua da makarantar firamare ta Daura kafin ya shiga Katsina Middle School a 1953.
Bayan nan, ya zarce Katsina Provincial Secondary School, tukunna ya shiga makarantar horarwa ta sojoji (NMTC) a 1962. Tsakanin 1962 da 1963 yaje Cadet Training dinsa a Mons Officer Cadet School a Aldershot dake Ingila.
Buhari yana daya daga cikin wadanda suka yi wa Yakubu Gowon juyin mulki, sakamakon haka aka daura shi a matsayin gwamnan jihar Borno na mulkin soji, wanda da ake kira jihar arewa maso gabas.
Sannan a wannan shekarar, janar Olusegun Obasanjo ya zabe shi a matsayin kwamishinan tarayya na man fetur.
Read Also:
A 1977, Buhari ya zama sakataren Supreme Military Headquarters. Sannan ya rike kwamandan sojoji na Kaduna.
An yi wani juyin mulki a 31 ga watan Disamban 1983, wanda aka daura Buhari a matsayin shugaban kasan Najeriya. Ya dauki tsauraran matakai akan masu karbar rashawa.
Buhari ya fara harkar siyasa ne a 2003, lokacin da yayi takara da Olusegun Obasanjo na shugabancin kasa, amma ya kayar dashi karkashin jam’iyyar PDP.
Ya kara tsayawa takara a 2007, amma Umaru Yar’Adua na PDP ya kayar da shi.
Sannan sun tsaya takara da Goodluck Jonathan a 2011, amma bai samu nasara ba. Sai a 2015 ne da ya tsaya takara karkashin jam’iyyar APC ya samu nasara.Ya zarce Jonathan da kuru’u miliyan 2.5. An nada shi a kan karagar mulki a 29 ga watan Mayun 2015.
Ya samu nasarar samun kuru’u 56%.
An karrama Buhari a wurare mabambanta, ciki har da Defence Service Medal (DSM), Congo Medal (CM), General Service Medal (GSM), Grand Commander of the Federal Republic of Nigeria ( GCFR), Global Seal of Integrity (GSO).
Buhari ya yi aurensa na farko ne a 1971, inda ya auri Safinatu Yusuf. Sun haifi yara 5, Zulaihat (marigayiya), Fatima, Musa (marigayi), Hadiza da Safinatu. Auren Buhari ya kare da Safinatu a 1988.
Ya auri matarsa ta biyu bayan rabuwarsa da ta farkon a watan Disamban 1989. Matarsa, Aisha Buhari, tana da yara 5, Aisha, Halima, Yusuf, Zahra da Amina.
Buhari yana daya daga cikin attajiran Najeriya. A 2021, an kiyasta cewa ya mallaki dala miliyan 110. Buhari yana daya daga cikin masu dukiyar kasar nan tun daga lokacin da yayi mulkin soji har zuwa yanzu.