Tarihin Rayuwar Shugaban Rasha Vladmir Putin Wanda ya Afka wa Ukraine

 

Da alama Shugaban Rasha Vladmir Putin ya bai wa mutane mamaki da ya afka wa Ukraine, wanda shi ne babban matakin soja da ya ɗauka tun bayan ƙwace yankin Crimea a 2014, amma fa bai taɓa ɓoye manufarsa ba ta faɗaɗa tasirin Rasha.

Mista ya kasance a kan mulki tun 2000 – a matsayin shugaba da kuma firaminista kuma shi ne shugaban da ya fi kowa daɗewa a Fadar Kremlin tun bayan jagoran kama-karya na Tarayyar Soviet Joseph Stalin, wanda ya mutu a 1953.

Wata ƙuri’ar raba-gardama da aka kaɗa a 2020 ta bai wa Putin damar ci gaba da mulki fiye da wa’adin mulkinsa na yanzu wanda zai ƙare a 2024. Saboda haka, zai iya ci gaba da zama a mulki har zuwa 2036.

Amma ta yaya ya zo nan? Ga bayanai game da harkokin siyasa da rayuwar mutumin da a yanzu duk duniya ke ta magana a kansa.

Tsohon jami’in leƙen asiri
Masu sukarsa na kallon rayuwar Putin a matsayin wadda ta samo asali daga shekarun aikinsa a lokacin Tarayyar Soviet.

Mai leƙen asiri ne a hukumar KGB – gawurtacciyar hukumar leƙen asiri ta Tarayyar Soviet – kafin ya yi nasarar zama wani a lokacin da USSR (Soviet) ke tsaka da wargajewa.

Da yawa daga cikin na kusa da shi ko kuma hadimansa na gwamnati suna da alaƙa ko kuma sun yi aiki da hukumomin leƙen asiri.

Mista Putin ya fara harkokin siyasa a shekarun 1990, lokacin da ya yi aiki a matsayin babban mai taimaka wa magajin garin St Petersburg Anatoly Sobchak, wanda ya koyar da shi harkokin lauyanci a jami’a.

A 1997, ya shiga Fadar Kremlin a matsayin shugaban hukumar tsaro ta ƙasa wato Federal Security Service (FSB – wadda ta maye gurbin KGB) kuma ba daɗewa aka ayyana shi a matsayin firaminista.

A jajiberin sabuwar shekarar 1999, Shugaban Rasha Boris Yeltsin ya sauka daga mulki kuma ya naɗa Putin a matsayin Muƙaddashin Shugaban Ƙasa.

Tun daga wannan loakci yake kan mulki, duk da cewa ya riƙe muƙamin firaminista daga 2008 zuwa 2012 saboda kundin tsarin mulkin ƙasar ya hana shi yin takara karo na uku a jere.

Ya sake komawa kan mulki bayan lashe zaɓen 2012 da kashi 66 cikin 100 duk da zargin maguɗi.

Ya sake dawo da salon mulkin Tarayyar Soviet yayin faretin sojoji, kuma hoton Shugaba Stalin, wanda a baya aka haramta, ya sake bayyana.

Hatta rigakafin korona da Rasha ta ƙirƙira sunansa Sputnik V, wanda sunan wani binciken Rasha ne da ya zama tauraron ɗan Adam na duniya a 1957.

Mista Putin ya kwatanta rushewar Tarayyar Soviet da cewa “mafi girman bala’in da ya faru a ƙarni na 20” kuma ya sha sukar salon ƙungiyar tsaro ta Nato kan ƙara faɗaɗa da take yi har zuwa kusa da iyakar Rasha tun daga 1997.

Ƙawance maras daɗi da ƙasashen Yamma
Rikci tsakanin Rasha da Ukraine da kuma shiga yaƙin Syria da Rasha ta yi wajen goyon bayan Shugaba Bashir al-Assad sun sake tayar da zargin da ƙasashen Yamma kan Mista Putin.

Alaƙa tsakaninsu ta ci gaba da kasancewa maras daɗi kamar a lokacin Yaƙin Cacar Baka. Sai dai an samu zakka ɗaya – Donald Trump ya bayyana abotarsa ƙarara da Putin.

A gefe guda kuma, wanda ya gaji Trump, Shugaba Joe Biden ya siffanta Putin a matsayin “makashi”.

Ƙaunar mazantaka
Mista Putin na son nuna kan sa a hotunan da ke nuna shi a matsayin namiji, inda ya shiga yankin Chechnya a cikin jirgin yaƙi a 2000 da kuma bayyana a taron matuƙa babur na Rashawa a tafkin Black Sea a 2011.

Maris 2013: Mista Putin kenan yake wasa da karnukansa a cikin ƙanƙara a wajen birnin Moscow

Wani binciken jin ra’ayin jama’a da cibiyar Russian Levada ta gudanar a Fabarairun 2021 ya nuna cewa kashi 48 cikin 100 na ‘yan Rasha na son Putin ya ci gaba da zama a kan mulki har bayan 2024.

‘Yan siyasar Yamma ba za su ji daɗin wannan adadin ba, ko kuma dai da yawa daga cikin mutanen na kallon Putin a matsayin mafi dama-dama.

Ya samu yabo saboda haɗa kan Rashawa da ya yi bayan rikicin tsarin kwamunisanci da ya faru a shekarun 1990.

Baya ga dawo da kishin ƙasa, Putin ya bai wa ma’aikata damar ci gaba da samun arziki, duk da yake da cewa birnin Moscow ne ya mamaye harkokin tattalin arziki kuma akwai talauci da yawa a ƙauyuka.

Tashin hankali a cikin gida

Mista Navalny wanda ke fama da rashin lafiya, an garƙame shi saboda wani tsohon zargin amubazzaranci. Wannan na cikin dalilan da ya sa alƙar Putin da Yamma ta ƙazanta.

Farin jinin da yake da shi a tsakanin tsofaffi a Rasha ya fi na matasa. Matasan masu yawa sun tashi ne a ƙarƙashin mulkinsa kuma da yawansu na neman sauyi.

Dubban matasan Rasha ne suka yi zanga-zanga a Janairun 2021 don nuna goyon bayansu ga jagoaran adawa Alexi Navalny, wanda ke sukar Putin kuma aka kama shi jim kaɗan bayan ya koma ƙasar daga Jamus.

Mista Navalny wanda ke fama da rashin lafiya, an garƙame shi saboda wani tsohon zargin amubazzaranci. Wannan na cikin dalilan da ya sa alƙar Putin da Yamma ta ƙazanta.

Yarinta mai tsauri

Mista Putin ya girma a wani gida maras daɗin zama da ke Leningrad – wanda yanzu yake a St Petersburg – kuma ya yi faɗa da yaran yankin da suka fi shi ƙarfi da girma. Wannan dalilin ne ya sa ya fara ƙaunar wasan kokawa na judo.

A cewar shafin Fadar Kremlin, Putin ya so ya yi aiki da hukumomin bayanan sirri na Soviet “tun kafin ya kammala makaranta”.

“Shekara 50 da suka wuce na koyi wata doka a titin Leningrad cewa idan faɗa ya zama dole to ka fara kai naushi,” a cewar Mista Putin a Oktoban 2015.

Ya yi amfani da kalamai masu tsauri na wani mai faɗa a kwararo wajen kariya daga hare-haren ƴan aware a Chechnya, inda ya sha alwashin kawar da su “ko da a cikin ban ɗaki suke.”

An bar Jamhuriyar Arewacin Caucasus da mafi rinjayenta Musulmai ne cikin halin ni ƴasu bayan mummunan faɗan da aka yi daga tsakanin shekarar 1999 zuwa 2000, inda dubban fararen hula suka mutu.

Georgia ta zamo wani wajen na rikici fa Mista Putin. A shekarar 2008 dakarunsa suka yi nasara a kan sojojin Georgia suka kuma ƙwace yankuna biyu da suka ɓalle – Abkhazia da South Ossetia.

Faɗa ne na ƙashin kai tsakanin sa da shugaban ƙsar Georgia na wancan lokacin mai goyon bayan ƙungiyar Nato Mikheil Saakashvili, ya kuma nuna shirin Mista Putin na yin barazana ga ƙasashen da ke ƙarƙashin Tarayyar Sabiyet a da masu goyon shugabannin yammacin duniya.

Abokai hamshaƙan attajirai
Ƴan tawagar Mr Putin hamshaƙan masu kuɗi ne kuma shi ma an yi amannar yana da ɗumbin arziki.

Amma ba ya bari a san harkokin iyalansa da na arzikinsa.

Takardun bankaɗa na Panama da aka sake a 2016 sun bankado wasu kamfanonin ƙasashen waje mallakar wani tsohon abokin Mista Putin – Sergei Roldugin.

Mr Putin da matarsa Lyudmila sun rabu a 2013 bayan auren kusan shekara 30. Ta bayyana shi a matsayin mayen aiki.

A cewar kamfanin dillancin labaran Reuters, ɗaya daga cikin ƴƴan Putin mata Katerina, tana da babban aiki a sahsen gudanarwa na Jami’ar Jiha ta Moscow sannan tana yawan shiga gasar raye-raye.

Ita kuwa babbar ƴarsa Maria, malamar jami’a ce wani fannin lafiya.

An yi waje da masu sassaucin ra’ayi
Salon kishin kasa na Mista Putin ya mamaye kafafen watsa labarai na Rasha, inda ake bayar da labarai da rahotanni na kusan abubuwan da suka danganci ra;ayinsa, saboda haka maganar masu hamayya kusan a ce babu ita.

A wa’adin mulkinsa biyu a matsayin shugaban kasa Mista Putin yana samun dukiya daga cinkin mai da gas, wadanda su ne manyan albarkatun da rasha ke fitarwa waje.

Yanayin rayuwar yawancin ‘yan kasar ya inganta, sai dai kuma wasu da dama na ganin kasar ta rasa dumukuradiyyarta da take tasowa.

Tun lokacin matsalar tattalin arziki ta duniya ta 2008 Mista Putin ke fama da tattalin arzikin da ya gamu da koma-baya sannan kuma a kwanan nan ga faduwar farashin mai a kasuwar duniya.

Rasha ta rasa masu zuba jari na waje da dama, wanda hakan ya haifar mata da kwashe dimbin kudaden da aka fice da su daga kasar.

Salon mulkin Mista Putin ya kasance ne na ra’ayin rikau na kishin Rasha, tare da goyon bayan akidar Kiristanci na gargajiya.

Jim kadan bayan da ya zama shugaban kasa Mista Putin ya fara nuna wariya ga masu ra’ayin sassauci a shugabancin kasar, yana maye gurbinsu da abokansa masu ra’ayin rikau ko kuma ‘yan ba-ruwanmu, wadanda galibi ake musu kallon ‘yan-amshin-shata.

Misali abokan Yeltsin kamar su Boris Berezovsky da Vladimir Gusinsky, dukkaninsu sun kare a matsayin ‘yan gudun hijira a waje.

International concern about human rights in Russia has grown over the years, following the jailing of oligarch Mikhail Khodorkovsky, once one of the world’s richest billionaires, and of anti-Putin activists from the punk group Pussy Riot.

Now, as Russian invades Ukraine and Putin warns that Moscow’s response will be “instant” if anyone tries to take on Russia – all eyes are the Russian president to see what he does next.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here