Yajin Aiki: A Taron NEC za a Bayyana Mataki na Gaba da za a Dauka – ASUU Reshen Legas
Da alama cewa malaman jami’o’i ba za su shiga yajin-aiki a ranar Talata ba.
A daren yau wa’adin da kungiyar ASUU ta ba Gwamnatin Tarayya zai cika.
Shugaban ASUU na jami’ar UNILAG yace sai ASUU tayi zaman NEC tukuna.
Lagos – Wani jami’in kungiyar ASUU yace malaman jami’a ba za su dauki matakin zuwa yajin aiki a ranar Talata, 31 ga watan Agusta, 2021 ba.
Jaridar Vanguard ta fitar da wannan rahoto a ranar Litinin, 30 ga watan Agusta, 2021.
Wani daga cikin ‘yan majalisar kolin NEC na ASUU, ya yi magana da Vanguard, inda ya bayyana cewa akwai matakai da ake bi kafin ayi yajin-aiki.
Read Also:
Dr. Dele Ashiru wanda shi ne shugaban reshen jami’ar Legas na UNILAG ya zanta da ‘yan jarida a ranar Litinin, yace wa’adin da suka bada yana nan.
Shugaban kungiyar na ASUU na UNILAG ya ke cewa sun ba gwamnatin tarayya zuwa karshen watan nan na Agusta domin a biya masu bukatunsu.
“Eh mun ba gwamnatin tarayya zuwa karshen watan nan, ta cika mana wasu daga cikin bukatunmu.”
Ba haka kurum ake soma yajin-aiki ba
“Amma ko da ba a cika mana bukatunmu a lokacin da muka bada ba, ba za mu fara yajin-aiki daga ranar ba.”
“Dalilin kuwa shi ne kungiyar ASUU ba ta mutum daya ba, kuma ba wani mutum guda yake da iko da ita ba.”
“A wajen taron NEC za a bayyana mataki na gaba da za a dauka. Yanzu haka ba a sa ranar yin zaman NEC ba.”