Tattalin Arziki: Kwamitin Majalisar Dattawa ta Fara Tattaunawa da Shugaban Babban Bankin Najeriya
Kwamitin hadin gwiwa na Majalisar Dattawa mai kula da harkokin kudi da Banki da Inshora da cibiyoyin hada-hadar kudi na Najeriya ya fara tattaunawa da jami’an babban bankin Najeriya (CBN) da Gwamnan bankin Yemi Cardoso ke jagoranta.
A ranar 31 ga watan Janairu ne dai kwamitin ya gayyaci gwamnan babban bankin kasar ya bayyana a gabansa.
Read Also:
Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake nuna damuwa kan halin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki da kuma faduwar darajar Naira a kasuwar canji.
Sanatocin sun bukaci babban bankin kasar na CBN ya yi bayani kan dimbin kalubalen tattalin arzikin da kasar ke fuskanta a halin yanzu.
Kasancewar talauci da rashin tsaro a kodayaushe sakamakon matsalar karancin abinci a ƙasar, ‘yan majalisar sun yi imanin cewa CBN ba zai iya gamsar da ‘yan Najeriya cewa manufofinsa suna aiki ba.