Rikicin Sudan: Babu Amfanin Tattauna Idan ba za a Tsagaita Wuta ba – Burhan
Ana ɗan samun takaitattun bayanai kan tattaunawar sulhu da Saudiyya da Amurka ke jagoranta kan Sudan a birnin Jeddah.
A ranar 6 ga watan Mayu aka soma wannan tattaunawa tsakanin ɓangaren Sojojin Sudan da dakarun RSF da ke tawaye.
Read Also:
Sai dai shugaban sojoji, Janar Abdel Fattah al-Burhan a jiya Litinnin ya shaida wa tashar talabijin din Masar na Al-Qahera cewa babu amfani wannan zaman tattaunawa ba tare da tsagaita wuta ba.
Janar Burhan ya jaddada cewa ba shi da wata damuwa kan kokarin da ake yi na ganin an kawo karshen zub da jini, sai dai ya nanata cewa wajibi ne RSF ta mika wuya ta ajiye makamanta.
Wani jami’in diflomasiyya na Saudiyya ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa har yanzu babu wani ci gaba da aka samu a zaman tattaunawar.