Tegina: Shugaban Makarantar ya Bayyana Halin da Daliban ke Ciki a Hannun ‘Yan Bindiga
Biyar daga cikin yaran makarantar Islamiyya ta Tegina da ke hannun ‘yan bindiga na cikin mawuyacin hali.
Shugaban makarantar, Abubakar Alhassan, ne ya bayyana cewa yan bindigan sun kirasa don sanar da shi halin da yaran ke ciki.
Hakan na zuwa ne bayan mutuwar wasu shida daga cikin daliban a baya.
Neja – Wadanda suka yi garkuwa da yaran makarantar Islamiyya ta Salihu Tanko sun bayyana cewa biyar daga cikin yaran da ke tsare suna cikin mawuyacin hali kuma suna iya mutuwa nan ba da jimawa ba.
Shugaban makarantar, Alhassan Garba Abubakar, ya ce masu garkuwar sun fada masa haka a hirar su ta karshe.
Masu garkuwa da mutanen, sun ce a shirye suke su karbi kudin fansa na farko na naira miliyan 18 domin sakin yaran ga iyayensu.
Amma gwamnatin jahar Neja ta yi watsi da sabon ci gaban a matsayin wata dabara da masu garkuwa da mutane suka shirya don samun karin kudi daga iyayen.
An bayar da rahoton cewa biyu daga cikin yaran da aka sace sun mutu a ranar Alhamis da ta gabata.
Read Also:
Alhassan ya ce ‘yan bindigar sun yi kiran gaggawa a waya, inda suka yi ikirarin cewa ba sa son wasu yaran su mutu, jaridar The Nation ta rawaito.
Ya ce:
“Sun kira ni kuma sun ba da labarin mutuwar. Sun bukace ni da in gaggauta domin a saki yaran domin biyar daga cikinsu suna cikin mawuyacin hali.
“Da mutuwar yara biyu da hudun farko da suka fara rasuwa, shida daga cikin yaran yanzu sun rasu duk da cewa mun biya Naira miliyan 50 a baya, muna addu’a a wannan karon Allah ya taɓa zuciyarsu ya sake su.”
Jaridar The Nation ta fahimci cewa iyayen sun sake fara tara kudi don hana ci gaba da mutuwar yaran su.
An tattaro cewa iyayen suna cikin damuwa game da wasanne daga cikin yaran ke cikin mawuyacin hali.
Amma Sakataren Gwamnatin Jahar Neja, Alhaji Ibrahim Matane, ya shaida wa jaridar cewa ‘yan fashin suna amfani da irin wannan dabarar don samun ƙarin kuɗi daga iyayen kuma a ƙarshe ba za su saki yaran ba.
Ya nemi iyayen da su kwantar da hankalinsu, yana mai ba da tabbacin gwamnati tana kan lamarin kuma za ta dawo da yaran cikin koshin lafiya.
Matane ya dage cewa matakin gwamnati na rashin biyan kudin fansa yana nan amma ya kara da cewa wannan ba yana nufin cewa gwamnati ba ta yin komai kamar yadda mutane da yawa ke gani ba.