Abu bakwai da Gwamnatin Shugaba Tinubu ta Cimma da Manyan ƙungiyoyin ƙwadagon Najeriya

 

Kimanin kwana ɗaya, ma’aikata a Najeriya su tsunduma yajin aikin da zai karaɗe faɗin ƙasar, saboda nuna fushi a kan matakin janye tallafin man fetur da sabuwar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta sanar, ƙungiyoyin ƙwadago sun dakatar da ƙudurin nasu.

Janye tallafin man fetur ɗin dai ya janyo farashin man ya yi tashin gwauron zabi a gidajen man fetur daga ƙasa da N200 zuwa kimanin N540.

Manyan ƙungiyoyin ƙwadagon Najeriya na NLC da TUC sun ce sun dakatar da shiga yajin aikin ne domin bayar da damar ci gaba da tuntuɓa da tattaunawa da sabuwar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

Sanarwar dakatar da shiga yajin aikin ta zo ne bayan wani taro da ɓangarorin uku suka yi a daren jiya Litinin.

1. Ƙarin albashi

Gwamnatin Tarayya da ƙungiyar NLC da TUC sun amince da matakin kafa wani kwamitin haɗin gwiwa wanda zai yi nazari kan ƙudurin ƙara mafi ƙarancin albashi a Najeriya.

Haka zalika, kwamitin zai yi ƙoƙarin ɓullo da wani tsari da lokaci na yadda za a aiwatar da matakin.

Tun farko, ƙungiyoyin ƙwadagon sun yi ta kafa hujja da cewa ba za su lamunci janye tallafin man fetur ɗin ba saboda zai iya haddasa tsadar kaya da ayyuka a duk fannonin rayuwa a ƙasar, a lokaci guda ba tare da ƙara mafi ƙarancin albashi na N30,000 ga ma’aikata ba.

2. Bai wa ƙananan ma’aikata tallafi

Ɓangarorin uku sun kuma amince da yin nazari kan wani shirin ba da tallafin kuɗi da Bankin Duniya ke samarwa da kuma ƙudurin shigar da ma’aikata masu ƙaramin albashi cikin shirin.

3. Shirin mayar da motoci masu amfani da gas

Ƙungiyoyin NLC da TUC da kuma gwamnatin Najeriya sun amince su farfaɗo da shirin da tun farko suka amince da shi a 2021 na mayar da motoci masu amfani da iskar gas maimakon man fetur.

Kuma sun amince kan yadda za su ci gaba da tattaunawa don su daddale kan hanyar da za a aiwatar da shirin da lokaci.

4. Bunƙasa ɓangaren Ilmi

Ƙungiyoyin ƙwadago da gwamnatin tarayya sun cimma yarjejeniyar yin nazari game da batutuwan da ke kawo cikas wajen tabbatar da inganci a ɓangaren samar da ilmi.

Kuma za a gabatar da abubuwan da ake jin za su zama mafita wajen bunƙasa harkokin ilmi a Najeriya don aiwatar da su.

5. Gyara matatun man fetur

Ɓangarorin da suka yi tattaunawar sun kuma amince za su yi nazari tare da ɓullo da wani tsari domin kammala garambawul ga matatun man fetur na Najeriya.

Manyan matatun mai guda uku na Najeriya da ke Kaduna da Fatakwal da kuma Warri duk sun durƙushe a yanzu ba sa aiki, abin da ya sa ƙasar ke shigo da tataccen man fetur daga ƙasashen waje bayan ta sayar da nata ɗanyen man.

6. Gyaran titunan mota

Ɓangarorin da suka yi tattaunawar ta ranar Litinin sun kuma amince cewa gwamnatin ƙasar za ta ɓullo da wani tsari wanda zai tabbatar da gyara titunan da ke faɗin ƙasar da kuma faɗaɗa hanyoyin jirgin ƙasa a Najeriya.

7. Buƙatun TUC

An kuma amince a yayin tattaunawar cewa kwamitin haɗin gwiwar da za a kafa zai bi diddigin dukkan buƙatun da ƙungiyar ƙwadago ta TUC ta gabatar wa gwamnatin tarayya.

Tun farko yayin wani taro da NLC ta ƙaurace masa a ranar Lahadi, ƙungiyar TUC ta gabatar wa gwamnatin tarayya wasu buƙatu daga ciki har da neman ƙara albashi mafi ƙaranci zuwa N200,000, sannan a mayar da farashin man fetur zuwa kuɗinsa na baya.

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com