EFCC za ta ɗaukaka ƙara kan Wanke Tsohon Shugaban Ma’aikata, Oronsaye Daga Zargin Cin Hanci

 

Hukumar da ke yaƙi da yi wa tattali arzikin Najeriya zagon ƙasar EFCC ta ce za ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin da wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke, na wanke tsohon shugaban ma’aikata na ƙasa daga zargin halasta kuɗin haram na wajen naira biliyan biyu da hukumar ke yi masa shi da wasu.

A wani saƙo da hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook, ta ce za ta ƙalubalancin hukuncin a gaban kotun ɗaukaka ƙara.

EFCCn dai na zargin Steve Oronsaye da mutunen da ake zarginsu tare da yin amfani da wasu kamfanoni wajen karkatar da kuɗin gwamnati ta hanyar amfani da kwangilolin bogi.

Yayin da yake watsi da ƙarar, alƙalin kotun mai shari’a Inyang Ekwo ya ce hukumar EFCCn ta kasa tabbatar da zarge-zargen da take yi wa mista Oronsaye.

To sai dai a cikin sanarwar da mai magana da yawun hukumar Wilson Uwujaren ya fitar ya ce alƙalin ya yi kuskure, saboda a cewarsa bai yi la’akari da shaidun da masu ƙara suka gabatar ba, a tsawon shari’ar, tare da bahasin da ɗaya daga cikin waɗanda ake ƙarar Osarenkhoe Afe ya furta da bakinsa a gaban kotun.

A shekarar 2015 ne hukumar EFFC ta gurfanar da Mista Oronsaye tare da shugaban kamfanin Fredrick Hamilton Global Services Limited, Osarenkhoe Afe da wasu kamfanoni uku bisa zarginsu da yin amfani da wasu kamfanoni wajen karkatar da kuɗin gwamnati ta hanyar amfani da kwangilolin bogi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com