Bola Tinubu ya Nuna Rashin Jindadin sa a Kan Hare-Haren da Ake Samu a Kasa
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Bola Tinubu, ya nuna fushin sa yayin da ake samun karuwar hare-hare kan al’umma a kasar.
Tsohon gwamnan na jahar Legas ya lura cewa wadannan hare-hare sun sa mutane da yawa sun raina rundunar tsaron Najeriya.
Tinubu, ya bukaci ‘yan kasa da kada su taba mika kai ga zargin juna Biyo bayan ci gaba da kashe-kashe da sace-sacen ‘yan kasa da ake zargin‘ yan fashi suna yi a fadin kasar, shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya mayar da martani.
A cikin sakonnin da ya wallafa a shafinsa na Twitter, @AsiwajuTinubu, a ranar Alhamis, 29 ga Afrilu, shugaban na APC ya ce ya damu da ta’addancin da zaluncin da ake kai wa mutane musamman a jahohin Borno, Yobe, Benuwai, Neja, da Imo.
Read Also:
Ya bayyana cewa hare-haren sun sa da dama sun yi watsi da sojoji da jami’an tsaron kasar da ke jefa rayukansu cikin hatsari don kare jama’a.
Da alama bai ji dadin yadda ake ta samun asarar rayuka ba, tsohon gwamnan na Legas, ya bayyana cewa dole ne gwamnati ta ci gaba da karfafa wa jami’an tsaro gwiwa don yin iya kokarinsu don shawo kan wannan barazanar.
Tinubu ya yi kira ga ‘yan Najeriya da kar su taba mika wuya ga jaraba na zargin juna duk da banbancin yanki ko addini.
Yayinda yake lura da cewa dole ne kowa ya hadu wajen yakar abokin gaba daya, tsohon gwamnan ya ce rashin jituwa zai kawo rashin nasara ne kawai.
Wannan na zuwa ne kwana daya bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya tattauna da Tinubu a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Buhari Sallau, mai taimakawa shugaban kasa na musamman kan kafofin yada labarai ya bayyana ta Twitter cewa sun yi ganawar ne a daren Litinin, 26 ga Afrilu.
Hadimin shugaban kasar ya bayyana cewa Bisi Akande, tsohon shugaban jam’iyyar na rikon kwarya, ya raka Tinubu a ziyarar.